Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kwamitin Tantance Makarantun Kiwon Lafiya masu Zaman Kansu a Katsina Na Ci Gaba da Ziyarar Gani da Ido Don Inganta Ingancin Ilimi


Kwamitin Tantance Makarantun Kiwon Lafiya masu Zaman Kansu a Katsina Na Ci Gaba da Ziyarar Gani da Ido Don Inganta Ingancin Ilimi 

A ranar Juma'a, 01 ga Nuwamba, 2024, Kwamitin Tantance Makarantun Kiwon Lafiya masu zaman kansu da aka dakatar a Jihar Katsina ya ci gaba da ziyarar gani da ido a makarantu daban-daban, karkashin jagorancin mai ba Gwamna shawara akan Cibiyoyin kiwon lafiya, Alhaji Umar Mammada. 

Wannan kwamiti da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kafa na da nufin tabbatar da cika dukkan ka'idoji kafin makarantun da aka dakatar su koma bakin aiki.

Kwamitin ya kai ziyara a makarantun kiwon lafiya dake karamar hukumar Funtua, ciki har da Muslim Community College of Health Sciences and Technology , College of Health and Environmental Funtua,Funtua Community College of Health Science and Technology. Manufar ziyarar ita ce a tantance ingancin kayan koyarwa, adadin malaman da suka dace da fannin da ake koyarwa, cika ka'idoji na ilimi, dakuman gwaje-gwaje da na nazari, da kuma yawan azuzuwa da yanayin gudanar da karatun dalibai.

Alhaji Umar Mammada ya bayyana cewa dalilin kawo ziyarar shine gani da ido game da hujjojin da makarantun suka bayar a satin da ya gabata a ma'aikatar lafiya domin tantance su.

Post a Comment

0 Comments