Header Ads Widget

Responsive Advertisement

mutanen da ambaliyar ruwa ya Shafa a Sabon Gari Zariya sun sami tallafi


mutanen da ambaliyar ruwa ya Shafa a Sabon Gari Zariya sun sami tallafi

Daga Fatima Umar, Zariya

A  yau ne Shugaban Karamar Hukumar Zariya Honorabul Engr. Jamil Ahmad Muhammad (JAGA), ya jagoranci rabon kayayyakin agajin da aka yi da nufin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa da ruwan sama ya shafa, da kuma daidaikun mutane da ke cikin matsananciyar bukata, inda sama da gidaje 100 a fadin karamar hukumar Sabon Gari suka ci gajiyar kayayyakin.

Waɗannan kayan agajin sun samu ne ta hannun kakakin majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya Rt Honorabul Abbas Tajudeen, PhD, ta hannun Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) Najeriya da Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA).

Kayayyakin sun haɗa da buhunan shinkafa kilogiram 25, buhun masara kilogiram 25, buhunan siminti, kwalayan kusan rufin, bokiti, man girki, daurin  zinc, murhun kananzir, kayan sawan maza da mata, da dai sauransu.

Shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon Shiek Abubakar Jamilu Albani Samaru Zaria, wanda mataimakin shugaban karamar hukumar Hon Abdulkareem Kamilu ya wakilta ya jaddada bukatar kafa kwamitin da zai tafiyar da aikin rabon kayayyakin tun daga farko har karshe, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka tabbatar ya samu waɗannan kayan agaji. Wannan hanya ta tabbatar da nasarar shirin da kuma bin ka'idojin rarraba.

Wannan shirin zai ci gaba da gudana a yau, in Allah ya yarda, ga wadanda abin ya shafa.

Da yawan mutanen da suka sami tallafin sun nuna jin daɗinsu tare da fatan Alheri ga wanda suka zama sanadi.

Post a Comment

0 Comments