Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kungiyar 'APC Arewa Youths Merger Group' ta yaba wa shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu

Kungiyar 'APC Arewa Youths Merger Group' ta yaba wa shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu


Kungiyar 'APC Arewa Youths Merger Group' ta yaba wa shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu bisa karbar korafinsu da kira da suka yi nasa akan ya sa saki yaran da aka tsare akan zanga-zanga  cikin awa 48.

A cikin wata sanarwa dake dauke da sa hannun jagoran Matasa na APC Arewa merger group  Hon Musa Mujahid ya sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai, ya ce sun yi matukar jin dadi da  farin ciki  game da yafe wa yaran da shugaban kasa ya yi  bayan amsa kira da suka yi  masa, ya kuma mika su hannun Gwamnonin jihohinsu wanda dama hakkin Gwamnonin ne su yi kokarin karbo su amma suka kasa aiwatarwa da haka ne.

Daga nan ya yi nuni da cewa musamman ma Gwamnan jihar Kano, wanda mafi yawan yaran 'yan asalin Kano ne, kuma shi ne ma ya bai wa Kwamishinan Shari'a na jihar umurnin a kai yaran kotu a hukunta su, amma ake neman a sa siyasa a maganar. Dole ne yanzu Gwamnatin Kano ta fito ta nemi gafarar wadannan yara da a dalilin matakin da ta dauka ne suka shiga wannan yanayi.

Kungiyar ta ce a lokacin da suka kai wa yaran  ziyara a inda ake tsare dasu sun kai musu tallafi na kayan abinci da na bukatun yau da kullum, sun yi musu alkawari dama a cikin awanni 48 za su nemi alfarma wajen shugaban kasa ya sa a sake su, kuma sun nema shugaban kasa ya amsa kiran nasu ya sa aka sake su.

Hon. Musa Mujahid Zantawa ya kara jaddada godiya ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a madadin matasan APC akan wannan shawara tasu daya dauka, hakan ya tabbatar da cewa shi  dan DimokwaraÉ—iyya ne ,sannan suna Æ™ara kira a gare shi ya É—auki nauyin karatun waÉ—annan yara da aka saki domin su zama masu kyakkyawar makoma nan gaba idan suka zama masu ilimi

Kuma sun yaba da dukkan jama'ar da suka nuna damuwarsu har aka sami nasara.

Post a Comment

0 Comments