Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kwastom Sun Bizne Buhunna 300 Na Gwanjo da suka Kama A Katsina

Yadda Kwastam ta binne Buhunna 300 na Gwanjo da suka Kama  jihar Katsina 

Daga Idris Umar, Zariya 

Hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa wato kwastom sun yi gangamin kwashe buhunan gwanjo fiye da 300 tare da bizne su a dajin Barawa da ke Katsina.

Kayayyaki da suka haɗa da dila 187 ta kayan gwanjo da buhunna 87 na gwanjon tare da ɗaurin Atampa 58 da suka kwashe fiye da shekaru huɗu da kamawa.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar da fara rufe kayayyakin shugaban hukumar kwastom a jihar Katsina, Abba Aji ya bayyana cewa sun  bizne waɗannan diloli ne domin inganta kiwon lafiyar ma'aikatan su.

" Waɗannan kaya sun fi shekara huɗu da kamawa, sun sha rana da ruwa har sun fara ruɓewa gashi suna wari, idan ba mu kauda su ba, suna iya cutar da lafiyar ma'aikatan mu." Inji shi 

A cewar shugaban hukumar kwastom ɗin sun nemi shawarar kwararru kafin yanke hukuncin bizne waɗannan kayayyakin, inda ya ce babu yadda za a yi a rabawa jama'a su musamman 'yan gudun hijira, saboda sun lalace.

Abba Aji wanda ya ce ya zama wajibi su yi amfani da shawarwarin masana da suka haɗa hukumar kula da muhalli ta ƙasa waje.n aiwatar da wannan aiki da ya ce zai taimaka wajen kiyaye lafiyar su baƙi ɗaya.

Post a Comment

0 Comments