Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gamayyar Kungiyar Manya da kananan Ma’aikatan jami'ar ABU Zariya Sun Shiga Yajin Aiki


Gamayyar Kungiyar Manyan Ma’aikatan jami'ar ABU Zariya Sun Shiga Yajin Aiki

Daga Idris Umar, Zariya 

A ranar Alhamis da ta gabata, mambobin ƙungiyoyin NASU da SSANU reshen Jami’ar Ahmadu Bello Zariya sun gudanar da zanga-zangar lumana a cikin harabar jami’ar, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ke jinkirta cika musu alkawurran da ta ɗauka tun 2009.

Zanga-zangar, wadda aka yi a ƙarƙashin jagorancin Kwamitin Haɗin Gwiwa (JAC), na cikin irin matakan da ake ɗauka a dukkan jami’o’in Najeriya domin matsa wa gwamnati lamba ta biya haƙƙoƙin da ake bin su.

Kwamared Mohammed A. Yunusa, shugaban ƙungiyar JAC na jami’ar, ya ce sun gaji da zaman jiran alkawurra marasa tabbas daga gwamnati. Ya bayyana cewa akwai albashin watanni biyu da aka rike musu, da kuma kudaden alawus na aiki da aka amince da su tun da dadewa amma har yanzu ba a biya su gaba ɗaya ba.

A cewarsa, gwamnati ta ce za ta biya naira biliyan 50 a matsayin earned allowances, amma yanzu haka sai naira biliyan 10 kacal aka biya. Haka kuma, an ki biyan wasu kaso na arrears na albashi da ya kai 25% da 30%.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga ginin Majalisar Jami’a zuwa babban ƙofar shiga jami’ar, suna ɗauke da takardu da rubuce-rubuce masu ɗauke da saƙonni kamar:
"Mun gaji da rashin cika alƙawari", "Ku biya mana albashin da kuka rike", da "Jinkirin da ake mana rashin adalci ne."

Kwamared Yunusa ya ce, idan har ƙungiyar ta ƙasa ta bayar da umarnin dakatar da aiki gaba ɗaya a jami’o’in Najeriya, to su ma za su bi umarnin nan take, ba tare da jinkiri ba.

Wannan na zuwa ne a wani lokaci da ake fuskantar ƙalubale da dama a harkar ilimi a Najeriya, lamarin da ke barazana ga ci gaban manyan makarantu a ƙasar.
Masu lura da al'amuran yau da kullum suna ganin wannan lamari bai dace a rinƙa samun irin hakanba a tsakanin gwamnati da kungiyoyi  Musamman yadda Allah yayiwa Najeriya arziki ta bangarori daban daban.

Yanzu dai ya'yan kungiyar su ɗauki wannan mataki ne a matsayin gargaɗi ga gwamnati.

Duk da yake sunyi zargin gwamnatin bata girmama alƙawari duk da kimar da take dashi a fuskan duniya.

Post a Comment

0 Comments