Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Sarkin Zazzau Ya Jaddada Kudurin Majalisar Masarauta Na Kare Hakkin Kowace Al’umma


Sarkin Zazzau Ya Jaddada Kudurin Majalisar Masarauta Na Kare Hakkin Kowace Al’umma

Daga Idris Umar,Zariya

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada cewa majalisar masarautarsa za ta ci gaba da jajircewa wajen kare hakkin kowane al’umma da ke cikin masarautar Zazzau.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar korafe-korafe daga Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Kasuwar Sabon Gari da kuma Ƙungiyar Masu Gyaran Mota ta Ganuwa a Zariya.

Ya bayyana cewa babban aikin majalisar masarauta shi ne tabbatar da adalci da kuma sauraron kowane bangare domin shawo kan matsaloli ta hanyar zaman lafiya.

“Ina kira ga masu ƙorafi da su rika adana takardu da shaidu da za su taimaka wajen warware matsalolinsu,” in ji Sarkin.

A nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Sabon Gari, Alhaji Adamu Ibrahim Alolo ya koka kan yadda kwamitin kula da kasuwar tare da wani kamfani mai zaman kansa da ke kula da kasuwar ke karya yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da Ƙungiyar.

Ya bayyana batun mallakar shaguna da rashin tsaro a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke ci gaba da addabar ‘yan kasuwar.

Alhaji Alolo ya roƙi Majalisar Masarautar Zazzau da ta sa baki, yana mai cewa Sarki uba ne ga kowa kuma suna neman  adalci akan abubuwan dake faruwa.

Shi ma shugaban Ƙungiyar Masu Gyaran Mota ta Ganuwa, Malam Tanko, ya nuna damuwa kan rahotannin da ke yawo cewa gwamnatin jihar Kaduna tare da wasu mutane na shirin mayar da su wani wuri a bayan Dutsen Kufena.

Malam Tanko ya bayyana cewa fiye da mutum 4,000 na dogaro da wurin don samun abin lura da iyali galibinsune  matasa masu koyon sana’a.

A cikin martaninsa, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi alkawarin tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki domin nemo mafita ta dindindin kan matsalolin da aka gabatar masa tare da kira ga dukkan ɓangaren da su zauna lafiya da juna.

Post a Comment

0 Comments