Ina Mika Godiya Ga Al’ummar Da Suka Zaɓi APC — Inji Sani Basawa
Daga Idris Umar, Zariya
Honorabul Sani Ɗahiru Umar Basawa ya bayyana godiyarsa ga al’ummar da suka ba shi goyon baya tare da zaɓen jam’iyyar APC a zaben da ya gudana ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.
Yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a gidansa da ke unguwar Basawa ƙaramar hukumar Sabon Gari, Honorabul Basawa ya nuna farin cikinsa da yadda al’umma suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Ya fara da miƙa godiya ga mai girma Gwamnan ya Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da kuma Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Sheikh Abubakar Jamilu Albani, bisa goyon bayansu da ƙarfafa masa gwiwa.
“Hakika ban da iyayen jam’iyya, akwai malamai, sarakuna, matasa, mata da sauran jama’ar gari da suka nuna kishinsu da jajircewa wajen tabbatar da cewa zaɓe ya gudana cikin lumana. Ina mika godiya ta musamman gare su,” in ji shi.
Har wa yau, ya yaba da rawar da jami’an tsaro da malamai masu sa ido kan zaɓe suka taka, inda ya ce sun bayar da gudunmawa matuƙa wajen tabbatar da sahihancin zaben.
A ƙarshe, Honorabul Basawa ya bayyana cewa ƙofarsa a buɗe take ga kowa da kowa domin bada shawara da hadin kai a matsayin sa na wakilin al’umma. Ya roƙi gafara daga duk wanda aka ɓata masa rai ko aka sabawa a yayin fafatawar zaɓen.
“Ina roƙon hadin kan kowa da kowa domin ci gaban Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya. Allah ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji shi.
0 Comments