Header Ads Widget

Responsive Advertisement

AN KADDAMAR DA MASAUKIN BAKI NA ROYAL CHOICE A JAMI'AR AHMADU BELLO TA ZARIYA


AN KADDAMAR DA MASAUKIN BAKI NA ROYAL CHOICE A JAMI'AR AHMADU BELLO TA ZARIYA 

A yau Mai Martaba Sarkin Zazzau, shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna tare da Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Benuwai, TOR Tiv, Farfesa James Ortese Izuoa Ayatse, CFR  suka kaddamar da masaukin Baki na Royal Choice a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Cif Felex Tseado Akiga ya samar da wannan masaukin baki bisa tsarin Ginawa, Gyarawa tare da Gudanarwa. Har ila yau, wannan Masaukin Baki na hadin Guiwa ne tare da Jami'ar  Ahmadu Bello ta Zariya.
Daga cikin mahalarta bikin kaddamar da wannan masaukin Baki sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda da Ma'aikatan Shugabanin Jami'o'in Ahmadu Bello na Zariya da na Jos da sauran muhimman mutane duk sun halarci wannan biki.

Post a Comment

0 Comments