Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Water Aid ta kaddamar da rijiyar burtsatse kyauta a Hayin Dogo Samaru


Water Aid ta  kaddamar da rijiyar burtsatse kyauta a Hayin Dogo Samaru

Daga Idris Umar, Zariya

Wata kungiya da ta haɗa malaman jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ginawa al'ummar da ke anguwar Maƙera, Hayin Dogo Samaru, Rijiyar Tuka-tuka kyauta don rage masu wahalar rayuwa.

Wakilinmu ya halarci taron ƙaddamar da rijiyar ga al'ummar anguwar ta Maƙera, Hayin Dogo Samaru.

Dakta Hashim, wanda ya ke shi ne wakilin kungiyar, shi ne ya jagoranci bayar da gudummawar haƙa rijiyar.

Dakta Hashim ya yiwa manema labarai karin haske game da kungiyar tasu kamar haka, "Ita wannan kungiyar ta samo asali ne ta hanyar zumunci da ke tsakin malaman jami'ar Ahmadu Bello Zariya kuma muna ƙaunar juna a tsakanin mu. Bisa yadda muka ga al'umma na fama da matsalar rashin ruwa ya sa muka tuntubi junanmu tare da zartar da shawarar tara kuɗi a tsakanin mu don gudanar da taimako ga al'umma musamman a ɓangaren samar da ruwan sha ga al'ummar da muke tare dasu wannan, shine asalin wannan taimako da muke bayarwa."

Dakta Hashim ya tabbatar da cewa tuni kungiyar ta cigaba da gudanar da aikinta cikin aminci don haka ne ma a yau suke ƙaddamar da wannan rijiyar ga al'ummar anguwar Makera, Hayin Dogo samaru, jihar Kaduna.

Dakta Yusuf Ahmed Mu'azu yana daga cikin wadanda suke tafiyar da aiyukan wannan kungiyar mai suna "Water Aid", Daktan shima ya tofa albarkacin bakinsa game da lamarin a yayin kaddamar da wannan rijiyar, inda ya ce, "Gaskiya mun ji daɗi sosai kuma da ikon Allah zamu ci gaba da irin wannan gudunmawa ga al'umma don muma mu sami rabo duniya da lahira." Inda ya kara da cewa, "Mu ba 'yan siyasa bane, da kuɗin aljihunmu muke gudanar da wadannan ayyukan, wato daga albashin da muke samu duk wata. Ganin yadda ake fama da wahalar ruwan ne a cikin al'ummar da muke cikin su ne yasa muka yi  tunanin taimakawa jama'a, don haka mun godewa Allahu a yau gashi muna kaddamar da rijiyar ga al'ummar domin Allah."

Shima Dakta() kira ya yi ga mutanen anguwar da su kula da ita rijiyar don amfanarsu kuma ya roki jama'ar da su yi masu addu'a don samun ladar aikin da suke yi.

Hajiya Rakiya Shuaibu wace take zaune a anguwar a nata jawabin ta yi godiya ne ga ƙungiyar ta Water Aid, sai ta yi fatan Allah ya linka masu ladan aikin da suka yi duniya da lahira.

Malam Garba shine mai anguwar Makera Hayin Dogo, a nasa jawabin  shima cewa ya yi Allah ya sakawa duk wanda suka sanya hannu a wajan gina rijiyar, karshe ya yi alƙawarin sanya idanu wajan kula da rijiyar.

Cikin wadanda suka rufawa taron baya daga ɓagaren malaman jami'ar akwai Dakta S Musa Yahaya da Dakta Adam Tijjani, dukkansu kuma sun yi fatan alheri ne ga mutanen anguwar tare da nuna goyon baya wajan kulawa da rijiyar musamman yadda aka kashe kudi masu yawa wajen gina ta tare da amfani da ingantattun kayan aiki.

Malam Hassan matashi ne a anguwar ta Maƙera Hayin  Dogo Samaru, shima cewa ya yi sun gode da wannan kokari kuma zasu kula da wannan aikin da ikon Allah.

Limamai da masu anguwanni ne suka sanya albarka tare da yiwa malaman jami'ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya fatan alheri.

Post a Comment

0 Comments