Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Taron karawa juna sani ga Hakimai da Dakaittai ya sami karɓuwa a Zariya


TARON KARA ILIMI BISA TAKAN GUDANARWA

Daga Ummul-kulsum Nuhu, Zariya 

A Dakin Taro na Otel din R&K na Zariya a yau  Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed NuMaihu Bamalli, CFR ya halarci bude  Taron Kara Ilimi ga Dagatai da Masu Anguwannin na Gundumar Zariya Da Kewaye wanda Cibiyan Green Horizon ta shirya.
Wannan Kara Ilimi wanda Hukumar Ci Gaban Kasashe Rainon Ingila (FCDO) take tallafawa  zai kasance ne a bisa Sanin Hanyoyi Gabatar da Sassantawa gami da Sulhu a cikin al'umma. Kuma yana tafiya ne cikin shiyyoyi guda biyu mai dauke da Mahalarta Arba'in-Arba'in a kowace shiyya.
Shiyya ta Farko dai ya dauke ne da mahalarta daga Gundumar Zariya da Kewaye a inda Shiyya ta Biyu kuma mahalarta daga Gundumar Rigacikun suke halarta.
Farfesa Muhammed Tabi'u SAN da Balarabe Bello Kuliya sun gabatar da bayanai a lokacin bude wannan taro na yau.

Post a Comment

0 Comments