Shugaba ƙasa ya kafa Kwamitin Shirya Jana’izar Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Ummul-kulsum Nuhu,Zariya
Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wani kwamiti na ministoci don shirya jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin London a ranar Lahadi yana da shekaru 82.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a, Segun Imohiosen, ya fitar ta bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne zai jagoranci kwamitin, wanda aka dora wa alhakin tsara da kuma aiwatar da shirye-shiryen jana’izar da ta dace da girman marigayin shugaban kasa.
Mambobin kwamitin sun hada da ministocin Harkokin Kudi, Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Tsaro, Yada Labarai da Wayar da Kai, Ayyuka, Cikin Gida, Birnin Tarayya (FCT), Gidaje da Ci gaban Birane, Lafiya da Walwalar Jama'a, da kuma Harkokin Al’adu da Kirkira. Haka kuma, Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Darakta Janar na Hukumar DSS, da Babban Hafsan Tsaro suna cikin kwamitin.
Ofishin Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya (GSO) ne zai kasance a matsayin ofishin gudanarwa na kwamitin.
A wani bangare na nuna girmamawa ga marigayin shugaban kasa, Shugaba Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatun gwamnati da su bude kundin ta’aziyya a bakin kofofin ofisoshin su domin al’umma su samu damar yin addu’a da jajantawa.
Baya ga haka, an bude kundin ta’aziyya na musamman a Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma a cibiyar taro ta Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja domin jami’an diflomasiyya da sauran jama’a su yi ta’aziyya.
Ana sa ran ci gaban bayani game da shirye-shiryen jana’izar za su kasance a yayin da kwanaki ke kara tafiya.
0 Comments