Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari, marigayi shugaban Najeriya.
Tinubu ya sanar da haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.
"Kafin mu fara addu'o'i domin karrama Buhari, ina sanar da ku cewa mun sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari," in ji Tinubu.
0 Comments