Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta tsaurara Tsaro a Daura Domin Jana’izar Buhari


Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta tsaurara Tsaro a Daura Domin Jana’izar Buhari

Ummulkair- Nuhu, Zariya 

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta bayyana jimami da alhini game da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, inda ta aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina, al’ummar jihar da kuma daukacin ‘yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Bello Shehu, rundunar ta yaba da gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar wajen cigaban ƙasa.

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakan tsaro na musamman tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, karkashin jagorancin AIG na Yankin 14 da ke Katsina, domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin da za a gudanar da jana’izar a garin Daura, ƙaramar hukumar Daura, da kuma fadin jihar baki ɗaya.

“Rundunar ta dauki matakan tsaro domin tabbatar da doka da oda kafin, yayin da bayan kammala jana’izar,” in ji sanarwar.

Rundunar ta kuma yi addu’ar Allah Ya jikanta marigayin tsohon shugaban ƙasan

Post a Comment

0 Comments