Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamnatin jihar Katsina ta tausaya wa wanda sukayi haɗari da Gwamna zata biya kuɗin jinyarsu


Gwamnatin jihar Katsina ta tausaya wa wanda sukayi haɗari da Gwamna zata biya kuɗin jinyarsu

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana aniyarta na daukar nauyin dukkan kudaden jinya na mutane tara da hadarin mota ya rutsa da su a kusa da makarantar kimiyyar lafiya da ke Daura, wanda ya hada da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.

Hadarin ya afku ne da yammacin Lahadi, 20 ga Yuli, bayan da wata mota kirar Sharon Volkswagen ta yi taho mu gama da daya daga cikin motocin da ke cikin rakiyar gwamnan.

Babu wanda ya rasa ransa a lamarin, sai dai mutane biyu daga cikin fasinjojin motar Sharon sun samu karaya, yayin da sauran bakwai suka samu raunuka daban-daban. Dukkansu na karbar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Daura.

Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa duba marasa lafiyar a asibiti, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudaden jinyar da sauran bukatu da suka shafi lafiya.

“Kuma gwamnati za ta tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun samu cikakken kulawa ba tare da wata matsalar kudi ba,” in ji Dr. Zango.

Mutanen da abin ya shafa da kuma iyalansu sun bayyana godiya da jin dadinsu ga Gwamna Radda da gwamnatin jihar bisa irin kulawa da tausayin da suka nuna a gare su bayan hadarin.

Post a Comment

0 Comments