Header Ads Widget

Responsive Advertisement

An Fitar da Sunayen Ƴan Takarar da za su Shiga Zagaye na Ƙarshe kafin Shiga Musabaƙar Alƙur'ani ta Duniya


An Fitar da Sunayen Ƴan Takarar da za su Shiga Zagaye na Ƙarshe kafin Shiga Musabaƙar Alƙur'ani ta Duniya (Second Tasfiya).

A kwanakin baya, kwamitin tantace ƴan takara na musabaƙar Alƙur'ani ta duniya wadda Majlisu Ahlil Qur'an Initiative of Nigeria ta shirya kuma ta ɗauki nauyi ƙarƙashin Gwani Muhammad Adam Alƙali OON, kwamitin tantancewar ya kammala tantance ƴan takara zagaye na farko.

Cikin sanarwar dake ɗauke da sa hannun sakatare Dr. Gwani Yahuza Hussain Umar, kwamitin tantancewar ya sanar da sunayen ƴan takarar da suka yi nasara waɗanda suka fito daga jihohi daban-daban dake faɗin Nigeria.

Kwamitin tantancewar ya samu ƙarin ƴan takara guda (10) bisa sahalewar Center for Qur'anic Studies ta jami'iar Usman Dan Fodio Sokoto, wanda hakan ke nuna ƴan takara (30) ne za su shiga zagaye na biyu (second tasfiya).

Ƴan takarar za su shiga zagaye na ƙarshe wanda daga nan wanda ya samu nasara shi zai wakilci Nigeria a musabaƙar da za'a gudanar ta duniya a ƙarshen watan August.

Post a Comment

0 Comments