Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Sabuwar Jam’iyya Ta Ƙawancen 'Yan Adawa: Atiku Da El-Rufai Sun Nemi Rajistar ADA A Wajen INEC



Sabuwar Jam’iyya Ta Ƙawancen 'Yan Adawa: Atiku Da El-Rufai Sun Nemi Rajistar ADA A Wajen INEC

 Ƙungiyar Ƙawancen 'Yan Adawa ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta mika buƙatar rajistar sabuwar jam’iyya mai suna All Democratic Alliance (ADA) a gaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC)

Rahotanni sun nuna cewa INEC har yanzu ba ta amsa ko ba da takardar karɓar buƙatar rajista ga ƙungiyoyi sama da 100 da suka nemi a yi musu rajista ba, ciki har da ADA.

Wani daga cikin jagororin ƙungiyar ya koka cewa hakan na sabawa dokar zaɓe, wacce ke buƙatar hukumar ta tantance duk wata buƙatar rajista cikin kwanaki 90.

Post a Comment

0 Comments