Asibitin Koyarwa na ABU: Nasarori da kalubale a karkashin shugabancina – Farfesa Umdagas
Daga Idris Umar, Zariya
Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika a Zariya, ABUTH, wato Farfesa Ahmed Hamidu Umdagas, ya bayyana irin tarin nasarorin da ya samu a tsawon shugabancinsa, da kuma kalubalen da asibitin da ke fuskanta a yanzu. Shugaban ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wasu ba’adin ‘yan jarida ciki harda wakiliyarmu a ofishinsa dake asibitin.
Shugaban wanda aka nada shi a shugabancin asibitin tun daga 2019 zuwa 2023, inda aka sake yi yi masa nadi na biyu daga 2023 zuwa yau, ya jinjina wa ma’aikatan asibitin bisa goyon bayan da suke ba shi a ko da yaushe wajen kawo wa asibitin ci gaba. Farfesan ya dora ci gaban da aka samu a asibitin a matsayin ayyukan ma’aikata baki daya ba aikinsa shi kadai ba.
Farfesan ya ce; “ba ni ne na yi aikin da al’umma ke yabo na ba, aikin al’umma ne gaba daya. Ba ni kadai ke jagorantar asibitin ba, akwai sauran abokan aiki da muka hada hannu domin biyan bukatun al’umma da suka zo asibitin domin su samu waraka”, ya nusasshe.
Shugaban ya ci gaba da cewa a lokacin da ya zo asibitin a matsayin shugaba a 2019, asibitin na cikin wani hali na kalubale daban-daban. Ya ce; hakan ya sanya ya zauna da ma’aikata suka tsara yadda za su farfado da ayyukan asibitin da kuma gyara shi domin kawo masa ci gaba.
Daga nan ya zayyano wasu ci gaba da ya kawo wa asibitin, inda ya ce; “mun samar da sashen kula da hatsurra da bada agajin gaggawa. Kafin zuwa na a wuri guda ake, amma da muka zo muka raba. Kuma wurin a lokacin yana daukar majinyata kamar 70. Bisa wannan dalilin muka kirkiri ‘Sashen Bayar da Agajin Gaggawa na rashin lafiya’ da kuma ‘Sashen Bayar da Agajin Gaggawa na tiyata’”, ya tabbatar.
Ya ce; wadannan sashe biyu duk suna bayar da agajin gaggawa ne ga majinyata, inda ya tabbatar da cewa; daya na kula da bangaren masu lalurar hawan jini, ciwon suga, maleriya da sauran su. Sai kuma dayan sashen na kula da rashin lafiyar masu bukatar tiyatar gaggawa; “mun yi wannan tsarin bambantawar ne domin saukakawa. Domin nan asibitin koyarwa ne”, in ji shi. Ya kuma kara da cewa; “A yanzu za mu iya lura da akalla bayar da agajin gaggawa ga majinyata 100 a lokaci guda”, ya jaddada.
Ya bayar da misali da yadda aka kawo mutum 30 a lokaci guda da suka yi hatsarin mota gaba-gaba, kuma suka kula da su har suka warke. Wanda ya ce cikin su mutum guda ne kawai ya rasa ransa. “na jinjinawa ma’aikatan asibitin nan saboda cikin dare aka kawo su”.
Daga cikin nasarorin da ya kawo a asibitin ya ce; a yanzu a Nijeriya asibitoci guda biyu ne kawai suke da likitoci na dindindin a bangaren bayar da agajin gaggawa, wadannan asibitin sune asibitin koyarwa na jihar Legas, da kuma asibitin koyarwa na ABU. “kazalika mun kuma gina cibiyar lura da masu lalurar damuwa. Mun kammala shiri kafin karshen shekarar nan za mu bude shi. Ba za mu yi gaggawa ba. A nan ba mu da tarbiyyar yin gaggawar kaddamarwa ba tare da ci gaba da aiki ba. Muna son da an kaddamar a ci gaba da aiki”, ya lurantar.
Da yake ci gaba da zayyano nasarorin da ya kawo, shugaban ya ce; gwamnatin tarayya ta samar musu da ‘MRI Machine’ da farashinsa a wancan lokacin ya kai dala miliyan 1.2. Inda ya ce a yanzu idan za a siya wannan na’ura naira biliyan uku yake. “a asibitin nan muna da MRI guda biyu – da 1.5 da kuma 0.2. A asibitocin arewa gaba daya ba inda ake da irin wadannan kayayyakin na gwaje-gwaje. Sannan muna da ‘128 Slide City’, shima irin wannan ba irinsa a asibitin gwamnati a arewa sai a nan”, ya jaddada.
Kazalika, ya ce bangaren karbar haihuwa ma, sun inganta fannin, ya ce kuma duk wannan ya samu ne sakamakon taimakon da suka samu daga gwamnatin tarayya a lokacin tsohuwar ministan kudi, Zainab Ahmad Shamsuna.
“sannan mun kawo ci gaba ta fuskacin tsabtar asibitin. A da idan ka zo shigowa ko fita asibitin nan za ka ji yana wari, amma da na zo muka fara gyara ‘Sewage System’ na asibitin”, in ji shi. Sai dai ya tabbatar da cewa har yanzu ba su kammala aikin ba.
Shugaban ya ce; a Disambar shekarar 2019 bayan bincikensu, sun kiyasta cewa asibitin na da bukatar naira biliyan 11.2 domin a gyara shi ya dace da zamani. “a wancan lokacin mun samu naira biliyan 2.3 daga gwamnatin tarayya a Disambar 2019. A lokacin farashin dala yana kasa da naira 360. Amma a 2020 kudaden da aka ba mu, sai ya zama sakamakon tashin dala komai ya canja. Amma dai mun yi iya bakin kokarin mu mun yi wasu ayyukan”, ya nanata.
Sai dai ya ce sun yi nasarar siyan wasu kayayyyakin aiki da dama da suka kawo wa asibitin ci gaba. Inda ya ce yanzu ko cika sauran naira biliyan 9 gwamnati ta yi, kudin ba zai isa ba a kammala gyaran asibitin saboda canje-canje da aka samu daga 2019 zuwa yau.
Shugaban ya ce; asibitin koyarwa na ABU yana da rassa shida da ya hada da; Shika, Tudun Wada, Ban Zazzau, Sabon Gari, Yakawada, da kuma Sakatariyar Gwamnatin Tarayya.
Da yake bayyana irin matsalolin da asibitin ke fuskanta, ya ce bai wuce matsala daga masu kawo majinyata ba. Inda ya ce ba a kawo musu mara lafiya sai ya jigata, masu lura da shi kudinsu ya kare. Wanda ya ce wannan matsala ce; “saboda idan suka kawo su nan sai su rika tunanin kamar muna wani siddabaru ne mutum ya warke”, in ji shi. Ya ja hankalin al’umma akan cewa a rika kawo mara lafiya da wuri ba sai ya galabaita ba, kuma kudinsu kuma ya kare.
Dangane da kalubalen da suke fuskanta kuwa, ya ce babba daga ciki shi ne batun wutar lantarki. Domin asibitin na biyan akalla naira miliyan 70 duk wata na wutar lantarki banda kudin dizel da suke kashewa. Ya ce wannan dalilin ya sa ake karbar kudaden gudanarwa daga hannun majinyata duk da asibitin gwamnati ne. Ya ce; suna gudanar da asibitin ne yadda mutane za su iya biya.
Ya ce kalubale na biyu shi ne karancin ma’aikata da kuma kayayyakin aiki da na more rayuwa. Duk da ya ce a yanzu gwamnati ta sakin musu mara suna daukar ma’aikata lokaci bayan lokaci. “wani kalubalen shi ne bangaren ababen more rayuwa da jinkirin sakin kudi daga gwamnati, amma na san wannan bangaren gwamnati za ta warware shi”, ya lurantar.
Da ya dawo bangaren bunkasa jindadi da walwalar ma’aikata kuwa, shugaban ya ce; kafin zuwansa, ma’aikata da yawa na bin kudade kala-kala, amma zuwansa ya biya duka wadannan basussuka.
“sannan a lokacin da na zo ma’aikatan asibitin nan duka akalla 1840 ne. A lokacin muna da gadaje akalla 750 a iya Shika kawai banda sauran rassan mu. Akwai karancin ma’aikata. Da daddare ba ma’aikata sosai. Amma zuwa na, kowanne shekara gwamnati na ba mu damar daukar ma’aikata. A shekarar da ya gabata kawai, mun dauki ma’aikata 580 a bangarori daban-daban. Hakan ya bunkasa walwalar ma’aikata. A yanzu akwai ma’aikata da yawa a asibitin nan suna gudanar da aikinsu. A yanzu korafe-korafe a wurin ma’aikata ba kamar da ba”, ya tabbatar.
Da yake sake karin haske dangane da walwalar ma’aikata kuwa, ya ce; a shekarar da ya gabata kawai, ma’aikata da dama sun samu horaswa da halartar tarukan bunkasa kai daga aljihun asibitin. Sannan ya ce a yanzu akalla suna da gadaje 1000. “Idan aka kammala gyare-gyaren asibitin nan za a samu ci gaba sosai. Kuma mutane suma za su samu ci gaba da samun yawaitar masu zuwa”, ya ce.
Ya ce duk daga cikin nasarorinsa, ya samar da sashe na musamman ga masu hali da za su iya biya, wanda ya ce za su kammala gina shi kafin karshen shekarar nan.
Da yake tsokaci dangane da shirin gwamnatin tarayya na karbar masu haihuwa a kyauta, shugaban ya ce a asibitin tuni shirin ya soma aiki; “akwai tsarin duba rashin lafiya a kyauta na gwamnatin tarayya ga wasu cututtuka musamman ma ga masu haihuwa. Wannan shiri gwamnatin tarayya ne take daukar nauyinsa, kuma mun fara shi tun a watan Mayu. Daga farawa zuwa yanzu masu rasa ransu a yayin haihuwa sun ragu da kashi 90 a asibitin nan”, ya tabbatar.
A karshe ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa kokarinta. Inda ya ce a yanzu akwai ‘Cancer Centre’ da za a kawo asibitin wanda tuni an riga da an fitar da kudin.
0 Comments