An raka shugaban karamar hukumar Bakori zuwa Makwancinsa.
Da hantsin yau Talata ne aka gudanar da jana'izar shugaban karamar hukumar Bakorin jihar Katsina mai rasuwa, marigayi Honorabul Aminu Dan Hamidu a karamar hukumar Bakori.
Kamar yadda Jaridar Taskar Labarai ta ruwaito, an gudanar da jana'izar ne da misalin karfe 11:00 na hantsin yau, wadda babban limamin Bakori, Sheikh Sa'ad Sani Imam ya jagoranta kamar yadda addinin Islama ya tanadar, inda kuma aka raka shi makwancinsa na din-din-din.
Jana'izar ta samu halartar manya jami'an gwamnatin jihar Katsina, manyan 'yankasuwa, manyan Malamai, Sarakunan gargajiya da sauran al'umma daga yankuna da sassa daban-daban a fadin Nijeriya.
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai; Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, shugaban ma'aikata Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON), Honorabul Rabo Tambaya Danja, sakataren kungiyar kuma shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Honorabul Isah Miqdad AD Saude da sauran da yawa daga cikin shugabannin kananan hukumomin jihar.
Marigayin dai ya rasu ne a daren ranar Litinin din da ta gabata bayan gajeriyar jinya, sannan kuma aka yi mashi sutura da rufe shi a yau Talata.
Allah ya jikansa da rahama, mu kuma Allah ya kyauta tamu tafiyar idan lokaci ya yi.
0 Comments