Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ya mike tsaye a kan Uba Sani


Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ya mike tsaye a kan Uba Sani

Daga Idris Umar, Zariya 

Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Honorabul Jamilu Abubakar Albani, ya yi kyakkyawan yabo ga Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa jajircewarsa wajen ci gaban ilimi a jihar.

Har wala yau ya bayyana gwamnan a matsayin “shugaba mai hangen nesa wanda tsarin mulkinsa na haɗin kai ke kawo sauyi a rayuwar al'umma a faɗin jihar Kaduna."

Honorabul Albani ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 14 ga Mayu, 2025, a lokacin ƙaddamar da shirin tallafa wa ɗalibai ta hanyar biya musu kuɗin jarabawar NECO da NBAIS da aka gudanar a ɗakin taro na Hukumar Alhazai, dake hedikwatar ƙaramar hukumar ta Sabon Gari.

Taron an shirya shi ne domin tallafa wa ɗalibai 350 daga makarantu daban-daban na sakandare a yankin ta hanyar rabon fom ɗin jarabawar NECO da NBAIS kyauta – wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin da ƙaramar hukumar ke yi wajen bunƙasa ilimi.

“Wannan rana ce ta tarihi ga fannin ilimi a Sabon Gari,” in ji Honorabul Albani. “Duk wani ci gaba da muke samu a wannan matakin yana samuwa ne saboda hangen nesan mai girma Gwamna Sanata Uba Sani. Shi ne ginshiƙin nasararmu, kuma da alfahari nake bayyana cikakken goyon bayana ga burinsa na sake tsayawa takara.”

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma buƙaci jama’ar jihar Kaduna da su ci gaba da marawa gwamnatin Gwamna Sani baya, wanda ya bayyana da cewa “gwamnati ce ta haɗa kai, ci gaba, da ƙarfafa gwiwa.”

A yayin da yake lissafa wasu daga cikin manyan ayyukan da aka aiwatar a Sabon Gari, Honorabul Albani ya ambaci ayyukan gina hanyoyi a unguwannin Hanwa, Palladan, da Basawa, da kuma bayar da tallafin karatu ga ɗalibai a gundumomi goma sha ɗaya na Sabon Gari da Basawa. “Ayyukan Gwamna Sani a fili suke kuma abin yabo ne,” in ji shi.

Ya kuma sake tabbatar da ƙudurin ƙaramar hukumar wajen taimaka wa ƙoƙarin gwamnatin jiha, musamman a fannin ilimi da ƙarfafa matasa.

A wata hira da aka yi da shi jim kaɗan bayan taron, Hon. Albani ya bayyana cewa jajircewar Gwamna Sani wajen ci gaban ilimi ne ya zaburar da shi har ya ƙaddamar da wannan shiri. “Abin da ya fi burge ni shi ne yadda Gwamnan ya rage kuɗin makaranta a makarantun gwamnati, lamarin da ya ba yaran da ba su da hali damar samun ilimi,” in ji shi.

Ya jaddada muhimmancin shugabannin ƙananan hukumomi wajen mara wa hangen nesan Gwamnan baya: “Yayin da Gwamna ke aiki a matakin jiha, dole ne mu ma mu taka rawar gani a matakin ƙasa.”

“Burinmu shi ne mu ɗaga darajar rayuwar al’ummar Sabon Gari. Wannan shiri a matakin farko ne,” ya jaddada. 

Honorabul Albani ya kuma bayyana wasu daga cikin ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa: “An kammala hanyar daga Yan Goro zuwa Hanwa; saura fitilar titi. Sauran ayyuka na ci gaba a unguwanni irin su Unguwan Gabas da wasu yankuna.”

A ɓangaren tsaro, ya yaba wa Gwamnan bisa sauya halin da ake ciki a wurare da suka haɗa da Giwa da Birnin Gwari, inda ya ce yanzu wuraren sun fi aminci kuma ana iya shiga kai tsaye.

“A Sabon Gari, ba mu da abin cewa illa yabo ga Uba Sani. Zuwa 2027, zai samu ruwan ƙuri'u cikin sauki,” in ji shi ya faɗa cikin ƙwarin gwiwa.

Ya bayyana Gwamna Sani a matsayin “mutumin al'umma” wanda ke fifita yankunan karkara da waɗanda ke cikin ƙunci. “Daga aikin gwamnatin tarayya da muka fara tun kafin gwamnatin tarayya ta shiga, zuwa ayyukan da muke shirin aiwatarwa da haɗin gwiwarsa – ciki har da Asibitin LIMI – zan gayyaci ’yan jarida da masu ruwa da tsaki domin shaida ci gaban da aka samu a aikin,” ya nusasshe.

Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin sun nuna farin cikinsu, inda suka nuna godiyarsu ga gwamnan da shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan tallafi.

Ɗaliban makarantar sakandare ta gwamnati da ke Hanwa da Jama’a sun shaida wa manema labarai cewa: “Gwamna Uba Sani da Shugaba Albani sun ba mu fata. Wannan bai tsaya kawai a taimakon kuɗi ba – abu ne da ke ƙarfafa mana guiwa mu ƙara ƙoƙari.”

Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi, shugabannin siyasa, da na gargajiya, da kuma Malaman addini, inda dukkansu suka yaba da wannan ci gaba wajen inganta makomar ilimin matasa a Sabon Gari.

Post a Comment

0 Comments