Jawabin Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a yau Alhamis I/5/2025
Yau na haɗu da abokaina, manyan ma'aikatan Najeriya, da abokan gwagwarmaya a fagen kare hakkin ɗan adam da dimokuraɗiyya, domin murnar Ranar Ma'aikata ta Duniya a Dandalin Murtala, Kaduna. A wajen wannan taro mai armashi da cike da launuka, mun girmama gudunmawar da ma'aikatan Najeriya suka bayar wajen neman 'yancin Najeriya, bunƙasa dimokuraɗiyya da tattalin arziki, da kuma ci gaba da fafutukar neman kyakkyawan yanayin rayuwa da aiki ga ma'aikatan ƙasar nan.
Gwamnatin da nake jagoranta za ta ci gaba da fifita walwalar ma’aikata tare da basu kayan aiki daidai da abin da ake da shi, tare da sanin cewa ma’aikata masu ƙwazo da shauƙi na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burinmu na sauya rayuwar yankunan karkara. Zuba jari a bangaren ci gaban ɗan adam da rage talauci zai ci gaba da samun kulawar gwamnati, ta hanyar zuba jari a fannin ilimi, lafiya, noma, gidaje, ƙanana da matsakaitan masana’antu, da kuma tallafawa hukumomin tsaro wajen yakar ta’addanci, 'yan fashi, satar mutane da sauran laifuka.
Gwamnonin Najeriya, ƙarƙashin haɗin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Najeriya, na tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago na matakin tarayya da jihohi domin ƙirƙiro sabon albashi mai kyau kuma wanda kowa zai yarda da shi ga ma’aikatan jihohi da ƙananan hukumomi. A matsayina na ɗan gwagwarmaya kuma abokin ma’aikata, ba zan huta ba sai mun cimma matsaya kan sabon albashin da zai saka murmushi a fuskokin ma’aikatanmu.
Yayinda muke ƙara zage dantse a shirinmu na sauya rayuwar yankunan karkara da aiwatar da sabbin shirye-shirye don farfaɗo da tattalin arzikinmu, muna neman haɗin kai da cikakken goyon bayan ma’aikatan Jihar Kaduna. Ƙara ƙwazon aiki da zaman lafiya a masana’antu za su taimaka mana wajen farfaɗo da tattalin arzikinmu kuma su ba gwamnati damar tinkarar matsalolin tsaro da na ci gaba da ƙarfi.
Sanata Uba Sani,
Gwamnan Jihar Kaduna.
1 ga Mayu, 2024
0 Comments