Rashin lafiyar Hauwa Adamu, bayan an je Asibitin Shika da ke Zariya...
-Ibraheem El-Tafseer
Game da rashin lafiyar Hauwa Adamu yarinya 'yar 3 da take fama da rashin lafiya a cibiya.
Bayan mun je Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu, sai suka tura mu Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya (Asibitin Shika), an isa Asibitin ranar Talata da yamma.
Bayan gwaje-gwaje daga likitoci har zuwa dare ana ta duba ta, sai suka ce sai ranar juma'a babban likitan da yake kula da wannan ɓangaren zai zo ya duba ta, sannan ya faɗi abin da za a mata. Aka zauna har zuwa ranar juma'a ɗin, da likita ya zo ya duba ta, aka mata gwaje-gwaje da dama. Sai ya ce za a mata aiki, amma sai bayan Sallah.
Aikin zai ci kuÉ—i daga dubu É—ari biyar (500,000) zuwa É—ari shida (600,000). Alhamdulillah akwai wani bawan Allah da ya ce ya É—auki É—awainiyar kuÉ—in aikin. Allah Ya saka masa da alheri.
Sai dai akwai batun magunguna da kuma abinci, Sannan da yake duk kwana ɗaya a asibitin kuɗi ake biya, ga wanda suka nuna cewa suna son su taimaka a wannan baiwar Allah, to har yanzu ƙofa a buɗe take ga duk mai niyyar yin musharaka a cikin wannan aikin taimakon rai.
Ga duk wanda zai iya taimakawa ga account number nan
2338520391
UBA Bank
Ibrahim Maitafsiri Sabo.
Ga kuma number É—in mahaifinta 0706 098 3164, 08025608283.
0 Comments