Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kamfaninmu na bin doka Inji --- Abba


Kamfaninmu na bin doka Inji --- Abba

A cikin satin da ya gabatane wakiliyarmu ya sami zantawa da wani matashi mai suna Abb Musa, mazauni garin  samaru Æ™aramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna akan yadda kamfanin sa ke gudanar da aiyukansa na sayan kayan nauyi( Gwangwani ) yanzu haka.

Abba yace muna samun ƙalubale masu yawa ta shigowar ɓata gari cikin sana'ar.

Yace bisa haka ne kamfanin sa yayi saurin daukar mataki don kare kansa daga shiga tarkon marasa gaskiyan.

Matashin yace sana'ar kayan nauyi sana'a ce mai albarka amma wasu ne marasa gaskiya suka shiga cikinta suka lalatata da takai ga duk inda ɗan (Gwangwani ya shiga sai a rinƙa mashi kallon mara gaskiya kuma abin ba haka yake ba.

Matashin yace a kowace sana'a ana samun masu gaskiya gefe guda a sami ɓata gari.

Bisa haka ne yace shi yanzu ya ɗauki matakin mai ƙarfi a kamfaninsa don magance matsalolin da sana'ar ke fuskanta.

Yace mataki na farko shine kamfaninsa baya siyan kaya sai da shaida mai karfin gaske.

Kuma ya tabbatar da cewa komin yawan kaya sai an tabbatar da gaskiyar sa kafin gabatar da cinikin sa wanda hakan yasa kasuwar sa na tafiya yadda ya kamata.

Karshe matashin yayi kira ga dukkan masu son shiga sana'ar kayan nauyi to ya fara da jin tsoron Allah ymkafin gudanar da sana'ar .

Matashin kuma yayi kira ga hukuma da su sanya ilmi yayin da suke yin aiki akan duk rahoton da suka samu akan ya'yan kungiyar tasu har ya kara da cewa domin ko wace sana'a akwai mutanan kirki akwai kuma mutanen  banza.

Ya kuma yi kira ga duk masu sana'ar kayan nauyi (Gwangwani) da suyi kokar suyi rijistar da uwar kungiya don magance matsalolin da ake fuskanta.

Post a Comment

0 Comments