Header Ads Widget

Responsive Advertisement

'Yan Nijeriya 39 suka rasu sakamakon zazzabin Lassa a cikin makonni uku


'Yan Nijeriya 39 suka rasu sakamakon zazzabin Lassa a cikin makonni uku 

Daga Abubakar Musa 

A cikin wani rahoto na halin da ake ciki wanda cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta wallafa ya nuna cewa mutane 39 sun rasu sakamakon zazzabin Lassa a cikin makonni uku na farko na shekarar 2025, kamar yadda wani rahoton kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ya nuna, mafi yawan mutanen da suka rasu din daga jihohin Edo da Taraba suka fito.

Zazzabin Lassa dai berayen da suka kamu ne ke yada shi.

Jihohin Edo da Taraba su suka fi kowa yawan wadanda suka rasu sakamakon cutar inda kowacce a cikinsu ke da mutane tara, sai Ondo da ke da mutane takwas da suka rasu, jihar Bauchi na da mutane hudu da suka rasu sai Ebonyi da ke da mutane uku da suka rasu.

Jihar Gombe ita ma tana da mutane uku da suka rasu; Kogi, mutum daya da ya rasu; Plateau, mutum daya da ya rasu; Nasarawa, mutum daya da ya rasu.

Jihar Edo na da mutane 266 da ake zargin sun kamu a cikin makonni uku na farko na shekarar 2025. Jihar Ondo na da wadanda ake zargin sun kamu mutum 250 a yayin da jihar Bauchi ke da mutane 154 da ake zargi sun kamu.

Taraba na da mutane 65 da ake zargin sun kamu, Ebonyi na da mutane 30 da ake zargin sun kamu, Gombe na da mutane 10 da ake zargin sun kamu, Nasarawa na da mutane 22 da ake zargin sun kamu sai kuma jihar Kogi da ke da mutane 9 da ake zargin sun kamu.

Kididdigar wadda hukumar ta NCDC ta fitar ta nuna cewa wadanda aka kula da lafiyarsu a cibiyoyin kula da lafiya sune 175, wadanda suka hadu da masu cutar sune 162, wadanda suka hadu da masu cutar da ake bibiya sune mutane 109 yayin da kuma wadanda suka hadu da masu cutar da aka kammala bibiya sune mutane 34.

Mafi yawan mutanen da cutar ta fi shafa sune mutane masu shekaru tsakanin 21 da 30.

Kamar yadda cibiyar ta NCDC ta bayyana, duk wani mutum da ke jin alamomi kamar rashin sanin takamaimai me ke masa ciwo, zazzabi, ciwon kai, ciwo a wajen makogo, tari, jiri, amai, zabin kirji, gudawa, rashin jin magana sosai, tarihin taba kashi ko fitsarin beraye da ciwon jiki zai iya kasancewa yana da zazzabin Lassa.

Post a Comment

0 Comments