Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Taron Hon Dahiru Magal Samaru yayi armashi


Taron Hon Dahiru Magal Samaru yayi armashi

Daga Idris Umar Zariya 

A safiyar Lahadi 8/2/25 ne Honorabul Ɗahiru Mangal, Samaru ɗan takarar kujerar majalisar wakilai wacce take wakiltar gundumar Basawa ya haɗa gagarumin taro don ƙarfara ya'yan jaɓiyarsu ta APC don saita wasuanufofinsa da haɗa kan ya'yan jama'ar a gundumarsa.

Taron an gudanar dashine a anguwar Yardorawa da ke hayin Dogo Samaru karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Wakilinmu ya halarci taron kuma ga yadda taron ya gudana.

Taron ya samu ƙarɓuwa ta ɓangaren manyan yan siyasar karamar hukumar Sabon Gari mata da maza.

A ɓangare guda kuma kungiyoyin matasa da sarakuna da limamai ne sukayi daffi don yin addu'a ga ɗan takarar bisa yadda yake gudanar da harkokin sa ba tare da ƙyamar kowa ba.

Bayan mayan baki sun gama gabatar da jawabi tare da nuna karamci ga ɗan takarar ne sai shugaban kungiyar ciyamomin na jihar Kaduna wato ALGON Chiarman Honorabul Abubakar Jamilu Albani yayi nasa jawabin.

Shugaban ya farane da godiya ga shugaban giji Allah ɗaya bashi damar zuwa wannan taro.

Kuma yayi kira ga ya'yan jaɓiyarsu ta APC dasu ci gaba da ƙokarin da suke yi na baiwa jamɓiyar APC goyon baya.

Karshe ya nemi haɗikai ga dukkanin jama'ar karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki ɗaya dasu ci gaba da baiwa Sanata Uba Sani goyon baya yace,da yardar Allah za a sami ci gaban rayuwa.

Shugaban ya baiwa taron gudummawa mai tsoka tare da yiwa jama'ar gurin fatan komawa gida lafiya.

Ganin yadda shugaban yayi a wajan taro sai mayan baki suka mara mashi baya tare da bayar da tasu gudummawar .

Shima wanda yayi gaiyatar Honorabul Ɗahiru Mangal,Samaru a yayin da yake nasa jawabin na godiya da kara da aka nuna mashi tare da rufe taron Magal ya nuna matukar godiya tare da jinjina ga dukkanin manyan bakin da suka zo wajan taron har yayi fatan in Allah ya bashi nasara zan ƙara kaimi wajan haɗa kan jama'ar gundumar Basawa don ci gaban rayuwarsu musamman matasa da iyaye mata.

Yace, zai kawo ci gaba a gundumar Basawa da ikon Allah.

 Yayi kuma fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Daga cikin manya baki a kwai Honorabul Abubakar Jamilu Albani da kansilolinsa da shuwagabannin jam'iyar mazaɓu da suka haɗa Bomo da Basawa da saura mazaɓun dake sabon Gari baki ɗaya.

Shaik Surajo Bomo ne ya ƙarkare da yin addu'ar neman samun nasara a tafiyar ta Honorabul Ɗahiru Mangal Samaru 

Anyi taro lafiya an tashi lafiya

Post a Comment

0 Comments