Shugaban ciyamomin jihar Kaduna Hon.Albani Samaru ya farantawa masu ƙananan sana'o'i rayuwa a ƙaramar hukumar Sabon Gari
Daga Idris Umar Zariya
A yau ne Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulki ta Sabon Gari
Kuma ALGON Chairman na Jihar Kaduna ya farantawa masu ƙananan sana'o'i rayuwa a yayin da ya bayar da tallafi a garesu.
Wakilinmu ya sami zuwa wajan da taron ya gudana.
Honorabul Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru a yau Laraba ne daruruwan mata masu ƙananan sana'a suka taru a babban gidan Honorabul Garba Datti Babawo dake GRA Sabon Garin Zariya a jihar Kaduna.
Taron matan ya kunshi amsa kirane tare da karbar tallafi na musamman daga shugaban na ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shugaban ciyamomin jihar Kaduna Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru.
Shugaban ya Ƙaddamar da rabon kayan sana'a ga sashin Iyaye “Mata” masu sana'ar suyar “Awara” domin Dogaro da kai.
A Yayin gudanar da taron.
Maigirma Shugaban Ƙaramar Hukumar ya tabbatar da tsarin zai ci gaba da gudana ta yadda za'a taɓa kowanne sashi na “Maza” da “Mata” masu sana'a a Ƙaramar Hukumar ta Sabon Gari.
Taron da ya sami halartar Maigirma Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari;
Hon Kamilu Abdulkareem (Ɗan Madami) da dukkan masu taimakawa Shugaban Ƙaramar Hukumar gurin gudanar da Ayyukan sa.
Bayan shugaban ya gama mikawa matan kayan tallafin tuni yayiwa wasu matan alƙawarin komawa dasu makaranta bisa tausayawar rayuwarsu
Wasu kuma yayi fatan duk lokacin da auren su ya taso zai bada nasa gudummawa .
Shugaban yayi roko ga matan da suka taho daga mazaɓu daban daban daga fadin ƙaramar hukumar ta sabon Gari da cewa kowa tayi kokari tayi sana'ar ta cikin kwanciyar hankali don kyautace ya basu ba bashiba.
Karshe shugaban yayi godiya ga Sanata Uba Sani Gwamnan jihar Kaduna bisa irin gudunmawar da yake basu don karfafa jama'a a fadin jihar Kaduna baki ɗaya yace, Wallahi babu abin da zamu ce masa sai fatan alheri da kariya ta Allah da muke fata gareshi.
Shugaban ya kuma yi alƙawarin ci gaba da wannan hidima.
Wata mata shohuwa mai suna murja daga anguwar Muciya da ta zama cikin wanda suka sami tallafin ta baiyanawa manema labarai cewa mijinta ya mutu ya barta da marayu da sana'ar Soya Awara take ciyar dasu har suje makaranta bisa haka ne tayi godiya ga ALGON Chiarman Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru bisa kara mata karfi da yayi a wannan rana.
Itama mama Hakima ta yaba sosai da wannan kokari na Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru na basu tallafi don ci gaban sana'ar su.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.
0 Comments