Mun shaida da kokari Hon Muktar Prince--Inji wakili
Daga A'isha Suleman Zariya
A cikin Satin da ya gabata ne ɗaya daga cikin wakilan al'umma dake gundumar Basawa a ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.
Wakili da aka fi sani da suna Alhaji Jume ya nuna goyon bayansa shi da jama'a da yake tare dasu ga ɗan takarar kujerar majalisar wakilai na jihar Kaduna wacce take wakiltar gundumar Basawa a ƙaramar hukumar Sabon Gari.
Wakili ya baiyana ra'ayinsa ne yayin da yake zantawa da manema labari a offishinsa dake makarantar UPE kallon kura Halin Dogo Samaru.
Wakili yace, yana daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a gudanar Basawa kuma shugaban a kungiyar iyaye na makarantar yara ta UPE hayin Dogo Samaru.
Bisa haka ne ya gano cewa ɗansu mai suna Honorabul Muktar (Prince) abin koyi ne ga al'umma baki ɗaya, saboda ƙokari da hangen nesa irin nasa.
Wakili ya ƙara da cewa a matsayin su na iyaye a wannan guguwar sun gamsu da fitowar Honorabul Muktar a matsayin ɗan takarar kujerar majalisar jihar Kaduna mai wakiltar gundumar Basawa a jamɓiya APC.
A cikin zantawar sa da manema labarai Malam Kabo ya zakulo wasu daga cikin gudummawa ayyukan da Honorabul Muktar Prince ya kawo masu a matsayin tallafi.
Wakili yace Honorabul Muktar ya kawo ma al'ummar kallon Kura tallafin magani kusan mutum Dubu ɗaya suka amfana da tallafin.
Wakili yace, shine matashi na farko da ya kawo irin wannan tallafin a wannan yankin.
Haka-zalika wakili ya ƙara tabbatar da cewa Honorabul Muktar ya kawowa ɗaluban ƙaramar makarantar Firamare dake nan kallon kura tallafin littafai ba sau ɗayaba hakan ya nuna shi a matsayin mai kishin jami'arsa.
Ƙarshe Wakili yayi kira ga gwamnan jihar Kaduna da Sanata Uba Sani da cewa in dai yana son wakilcin mai kyau tare da fita kunya to ga Honorabul Muktar Prince a gudanar Basawa ya fito takara a tallafa mashi.
Karshe yayi fatan Honorabul Muktar zai ci gaba da kokarin da yakeyi na taimakon al'umma.
Kuma yayi rokon jama'ar gundumar Basawa da ƙaramar hukumar Sabon Gari zasu marawa Honorabul Muktar baya don ya zama wakilin su a majalisar jihar Kaduna karkashin jamɓiyar APC .
0 Comments