Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Hon Muktar Prince yaron kirkine --- Cewar Kabo


Hon Muktar Prince yaron kirkine --- Cewar Kabo

Daga Fatima Idris Zariya 

A cikin Satin da ya gabata ne ɗaya daga cikin wakilan al'umma dake gundumar Basawa a ƙaramar hukumar Sabon Gari  jihar Kaduna.

Malam Kabiru Kabo da aka fi sani da suna Karkashe ya nuna goyon bayansa shi da jama'a da yake tare dasu ga ɗan takarar kujerar majalisar wakilai na jihar Kaduna wacce take wakiltar gundumar Basawa a ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Malam Kabo ya baiyana ra'ayinsa ne yayin da yake zantawa da manema labari a offishinsa dake makarantar UPE kallon kura Halin Dogo Samaru.

Malam Kabo yace, yana daga cikin shugabannin kungiyar iyayen yara na SBMC a UPE kallon kura.

Bisa haka ne ya gano cewa ɗansu mai suna Honorabul Muktar (Prince) abin koyi ne ga al'umma baki ɗaya, saboda ƙokari da hangen nesa irin nasa.

Kabo ya ƙara da cewa a matsayin su na iyaye a wannan guguwar sun gamsu da fitowar Honorabul Muktar a matsayin ɗan takarar kujerar majalisar jihar Kaduna mai wakiltar gundumar Basawa a jamɓiya APC.

A cikin zantawar sa da manema labarai Malam Kabo ya zakulo wasu daga cikin gudummawa ayyukan da Honorabul Muktar Prince ya kawo masu a matsayin tallafi.

Malam Kabo yace Honorabul Muktar ya kawo ma al'ummar kallon Kura tallafin magani kusan mutum Dubu ɗaya suka amfana da tallafin.

Malam Kano yace, shine matashi na farko da ya kawo irin wannan tallafin a wannan yankin.

Haka-zalika Malam Kabo ya ƙara tabbatar da cewa Honorabul Muktar ya kawowa ɗaluban ƙaramar makarantar Firamare dake nan kallon kura tallafin littafai ba sau ɗayaba hakan ya nuna shi a matsayin mai kishin jami'arsa.

Ƙarshe malam Kabo yayi kira ga gwamnan jihar Kaduna da Sanata Uba Sani da cewa in dai yana son wakilcin mai kyau tare da fita kunya to ga Honorabul Muktar Prince a gudanar Basawa ya fito takara a tallafa mashi.

Karshe yayi fatan Honorabul Muktar zai ci gaba da kokarin da yakeyi na taimakon al'umma.

Kuma yayi rokon jama'ar gundumar Basawa da ƙaramar hukumar Sabon Gari zasu marawa Honorabul Muktar baya don ya zama wakilin su a majalisar jihar Kaduna karkashin jamɓiyar APC .

Post a Comment

0 Comments