Anyi Jana'izar Alhaji Albabello mai kusa Zariya
Daga Idris Umar, Zariya
Dasafiyar wannan rana ta Talata 4-2-2025 , aka gabatar da sallar jana'izar Alhaji Bala mai Kusa mai (ALBABELLO TRADING COMPANY) wanda Allah yayiwa rasuwa jiya Litinin bayan yayi fama da jinya.
Sarkin Karaye dake jihar kano, da hakimai yan majlisan masarautan Zazzau bisa jagorancin wazirin Zazzau da dunbin al'umma ne suka halarci jana'izar wanda aka gabatar a filin Gaskiya Co-Operation dake gaskiya Tudun Jikun Zariya.
0 Comments