Header Ads Widget

Responsive Advertisement

LIKKAFARSA TA YI GABA




LIKKAFARSA TA YI GABA

ISA GIDAN 'Bakko,Zariya

A wannan makon ne,Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli,ya amince da na'din Wakilin Tarihin Zazzau Alhaji Shehu Ahmed a matsayin Wanda zai ri'ka ilmantar da duk Wani sabon Hakimi da aka na'da,ayyukan da aka 'dora ma sa.
Takardar tabbatar da wannan matsayin ga Wakilin Tarihin Zazzau,ta fito ne daga sakataren masarautar Zazzau Kuma Magatardan Zazzau Alhaji Yusuf Abubakar Hayatu da ya sa hannu a takardar.
Ayyukan da aka 'kara wa Wakilin Tarihin Zazzau Alhaji Shehu Ahmed sun ha'da shaida wa sabon hakimin ayyukansa da wajen zamansa a gaban Mai Martaba Sarkin Zazzau da Kuma wajen zamansa a ranakun Sallah da sauran lokutan bukukuwan Sallah.
Sauran ayyukan da Wakilin Tarihin Zazzau zai ilmantar da sabon Hakimi sun ha'da da Hakimin da ke gabansa da Kuma bayansa a ranar Sallah da ranar Hawan daushe da Kuma Hawan Bariki.
Kafin dai wannan aiki da Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya 'kara 'dora wa Wakilin Tarihin Zazzau,shi ne babban jami'in da ke kula da duk Wasu lamurra da su ka shafi Tarihin masarautar Zazzau da Kuma wuraren tarihi da su ke masarautar Zazzau Baki 'daya.
A zantawarsa da wakilinmu Wakilin Tarihin Zazzau Alhaji Shehu Ahmed,ya nuna Farin cikinsa da wannan aiki da Mai Martaba Sarkin Zazzau ya 'dora ma sa,sai ya yi addu'ar  ganin ya Sami taimakon Mai duka wajen sauke wannan aiki da Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya 'dora ma sa.
END.....

Post a Comment

0 Comments