Header Ads Widget

Responsive Advertisement

An kammala Zaben ƙananan hukumomi a jihar Katsina



An kammala Zaben ƙananan hukumomi a Katsina 

Daga A'isha Sunusi Ango Bomo Zariya

An bayyana zaben kananan hukumomin Jihar Katsina da aka kammala a ranar Asabar, 15 ga Fabrairu, 2025, a matsayin zaɓe da ya gudana cikin kwanciyar hankali.
An gudanar da zaben ne a dukkananan hukumomi 34 da mazabu 361 tare da cikakken sa-ido da kulawa.

Jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiya yayin zaben ta hanyar takaita zirga-zirga da kare tsaro a dukkan rumfunan zabe. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC) ta gudanar da aikin tantance masu kada kuri’a da kyau, inda aka tabbatar da ingancin katin zabe na dindindin (PVC) kafin a ba wa mutane damar kada kuri’arsu daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.

Bayan kammala kada ƙuri’a, an kidaya ƙuri’u a gaban jami’an tsaro, wakilan jam’iyyun siyasa, da ‘yan jarida. Daga nan ne aka tattara sakamakon gaba daya a hedikwatar KTSIEC, inda aka tabbatar da adadin kuri’un da kowace jam’iyya ta samu.

KTSIEC ta sanar da cewa dukkannin ‘yan takarar jam’iyyar APC ne suka lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, bisa la’akari da kuri’un da suka fi tarawa da cika ka’idojin da doka ta tanada.

duk da yake babbar Jam'iyar adawa ta PDP a Jihar  bata shiga cikin zaɓen ba bisa wasu dalilai nasu na ƙashin kai.

Wakilanmu sun  nemi jin ta bakin shuwagabannin jamɓiyun  adawar don jin ta bakinsu amma lamarin ya cutura bisa bin dokar jamɓiyar tasu.

A ɓangare guda kuma a daidai lokacin da ake gudanar da zaben Honorabul Shamsuddin Abubakar, Ciroman Danja ɗan majalisa mai wakiltar Danja ya shaidawa wakilinmu cewa sun gamsu da yadda zaɓen ya gudana har yayi fatan samun nasara ga jamɓiyar APC a dukkan matakai.


Shima Ma'ajin Jamɓiyar APC na ƙaramar hukumar Danja Alhaji Hamisu Malam godiya yayi bisa yadda jama'a suka bayar da goyon baya wajan gudanar da zaben ba tare da tashin hankaliba.

Shima Honorabul Ibrahim Adamu S K, Danja  ɗaya daga cikin iyayen jamɓiya ce a jihar Katsina  tuni ya nuna matukar jin daɗinsa bisa yadda zaɓen ya gudana ya kuma  jan hankalin dukkan wanda suka sami nasarar samun kujeru da suji tsoron Allah su taimakawa al'ummar da suke yace hakan zai sanya a sami nasarar abin da ake nema a gaba.

Post a Comment

0 Comments