Header Ads Widget

Responsive Advertisement

SABON TAMBARIN ƘARAMAR HUKUMAR KUDAN (LOGO)

Yau Litinin, 18/11/2024. Ƙaramar hukumar Kudan ƙarƙashin shugabancin Hon. Dauda Hunkuyi ta fitar da sabon tambarin ta (Logo) wanda ke ƙunshe da muhimman abubuwan da mutanen yankin ke yi, samarwa da fitarwa. 

Sabon tambarin ya fito da Sana‘ar Noma, tunda ga kan noman damina da na rani wanda shi ne sana‘a mafi shahara da al‘ummar ƙaramar hukumar Kudan ke yi. Kuma ya tabbatar da Kudan LGA a matsayin karamar hukuma dake kan gaba wajen noman zamani da samar da amfanin gona.

Duka wannan na ɗaya daga cikin hoɓɓasa na sabon shugaban ƙaramar hukumar Hon. Dauda na ganin an shigo da fasaha domin samun ingantaccen cigaba a karamar hukumar Kudan baki ɗaya.

Me zakuce?

Post a Comment

0 Comments