Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kaddamar da kungiyar tsaro a garin Bomo yayi armashi


Kaddamar da kungiyar tsaro a garin Bomo yayi armashi

Daga Idris Umar Zariya

Cikin nasara kungiyar ci gaban garin Bomo dake ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna ta ƙaddamar da wata kungiya mai suna Bomo Community Development Association security Corps wanda zata tsunduma cikin aikin kariya a cikin garin na Bomo da kewaye a cewar shugaban kwamitin tsaron Malam Liman Bello Bomo 

Ayayin da ake ƙaddamar da zaratan nasu kimamin mutum 100 ga dubban mutanen da suka halarci bikin yace, sun kaddamar dasu a matsayin ɗibar farko a wannan lokacin da yardar Allah za a ɗibi na biyu bada jimawaba.

A yayin ƙaddamar da rundunar tsaron wanda galibinsu matasane masu jini a jika sun gabatar da faretin na musamman ga bakin da suka halarci taron .

Bayan gabatar da ita rundunar tsaron ga manyan baƙi da sauran jama'a ne jagoran tafiyar ya faɗi nasarorin da rundunar ta samu daga kafata zuwa wannan lokacin.

Malam Bello shugaban rundunar ya tabbatar da cewa,daga kafa rundunar zuwa lokacin da ake yaye zaratan an sani raguwar aikata laifuka da dama a faɗin garin na Bomo da kewaye.

Shugaban yace tuni suka gabatar da sulhu masu yawa tare da samun nasarar janye wasu shara'o'i daban daban da mutane keyi a gaban kotuna mabanbanta.

Haka zalika shugaban rundunar ya tabbatar da ƙulla zumunci ga dukkan rundunonin tsaro da ake dasu a ƙaramar hukumar Sabon Garin baki ɗaya.


Ƙarshe yayi yabo na musamman ga Sarkin garin  Bomo Alhaji Muktar Salisu bisa basu goyon baya tun daga farko har ƙarshe lamari

Kuma ya mika soko na jinjina ga Santurakin Bomo Alhaji Lawal Jibirin bisa ɗaukar ɗawainiya mai yawa da bayar da goyon bayan da yasa aka sami nasara a kafa ita kungiyar.

Haka zalika ya jinjiwa shugaban kungiyar ci gaban garin Bomo malam Ɗahiru Tukur Muhammad bisa kokarinsa da azamarsa a dukkan abin da ya shafi ci gaban jama'a.

Daga karshen taronne shi Alhaji Lawal Jibirin Santurakin Bomo yayi jawabin ban girma ga dakarun da ƙwamandojinsu bisa yadda suka tsaya ƙyam har sai da aka sami nasara da aka samu.

Santurakin shima yayi godiya ga dukkan taƙwarorinsa da suka bayar da taimakonsu yace, hakan ya nuna cewa za a sami nasara a tafiyar baki ɗaya.

Ƙarshe ya tabbatar da cewa zasu ci gaba da bayar da gudummawa sosai don samun cigaba mai dorewa a dukkan ɓangarorin da ke tafiyar da rayuwar al'ummar garin Bomo da kewaye da ikon Allah.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments