Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Zuwa ga 'yan jarida.


Zuwa ga 'yan jarida.

'Yan jarida,musamman 'yan jarida matasa ku duba yadda 'yan fim ke kwace mana aiki.

Tallace tallace su ne,social media influencers sun karbe,kirkirar programs a TV da Radio sune,hulda da 'yan siyasa su ne..da sauran abubuwa da dama dake kawo kudi.

Shawara ta a gare ku,matasan 'yan jarida shine bayan aikin ku,ya kamata ku zama creative,kuma ku shiga wasu abubuwan da 'yan fim suka kwace.Kada ku zauna kawai sai dan albashin da gidajen da ku ke aiki ke biyan ku.Rayuwa kullum tsada ta ke karawa.

A matsayin ka na dan jarida za ka iya zama social media influencer har ka kai monetization level,za ka iya yin talla na products audio ko video,za ka iya neman sponsored political programs,za ka iya kikirar programs ka sayarwa DSTV da sauran su.Wani ka iya cewa sai da  jari...a fara da kadan sannu sannu sai a yi gaba.

Allah ya ba mu basira,mu yi amfani da ita.A dena yi mana kallon biyu ahu,mu dena bari 'yan fim na kwace mana aiki.Ko ana biyan ka da kyau ka kara kallon gaba.

Ina fatan wannan shawarar za ta taimaki ko da dan jarida matashi daya ne,ta sauya masa rayuwa.Ina fatan da yawa daga matasan 'yan jarida za su farka.

Post a Comment

0 Comments