Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Zargin cin zarafi: Shugaban sashin Hausa na BBC Aliyu Tanko ya yi murabus


Zargin cin zarafi: Shugaban sashin Hausa na BBC Aliyu Tanko ya yi murabus 

Babban Editan sashin Hausa na BBC mafi dadewa, Aliyu Tanko, ya yi murabus, bayan zarge-zargen cin zarafi da gallazawa daga tsohuwar ma’aikaciyar gidan, Halima Umar Saleh.

Da ya ke tabbatar da murabus ɗin nasa ga manema labarai, Aliyu Tanko ya ce ya yi murabus ne da bisa radin kansa bayan ya shafe shekaru 17 ya na yi wa BBC hidima cikin kwarewa.

Sai dai ya ʙi yin ʙarin bayani lokacin da manema labarai ke tambaye shi kan zarge-zargen “cin zarafi” da ke yawo a kafafen sada zumunta 

Wata majiya ta ce an aike da ʙorafe-ʙorafe masu yawa daga cikin gida da wajen gida zuwa hedikwatar BBC a Landan, suna neman a gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Ma'ajiyar jaridar DAILY NIGERIAN ta gano cewa Shugaban BBC West Africa, Ehizojie Okharedia, a ranar Laraba ya kira taron gaggawa, bayan haka ne Malam Tanko ya bar ofishinsa ba zato.

A matsayinsa na Shugaban BBC Hausa, malam Tanko ya jagoranci tawagar ’yan jarida a kasashe da dama.

Post a Comment

0 Comments