Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Zaben Cike Gurbi: Na ji dadin yadda ‘yan jam’iyyar APC suka fito, muna fatan lashe zaben, in ji Alhaji Sani SAS


Zaben Cike Gurbi: Na ji dadin yadda ‘yan jam’iyyar APC suka fito, muna fatan lashe zaben, in ji Alhaji Sani SAS

A yayin aka soma zaben cike gurbi na dan majalisar jiha na mazabar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna a ranar Asaba, daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a karamar hukumar Sabon Gari ya jinjinawa ‘ya’yan jam’iyyar.

Alhaji Muhammad Sani SAS, mashawarci na musamman ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Hon. Jamilu Albani ya nuna jindadinsa bisa yadda ‘ya’yan jam’iyyar APC suka fito kwansu da kwarkwatansu wajen kadawa jam’iyyarsu kuri’a a zaben cike gurbin da yake gudana.

Alhaji Sani ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a lokacin da yake zagayawa domin ganewa idonsa yadda zaben ke gudana.

A bisa haka ne, ya yi fatan cewa jam’iyyarsu ne za ta yi; “nasara a wannan zabe da ikon Allah”, in ji shi.

“wannan zabe ana gudanar da shi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, ga mutane sun fito sosai suna gudanar da zaben su”, ya tabbatar.

“Fatan mu kuma APC ce za ta yi nasara, ko yanzu aka tsaida kada kuri’a za mu ci zabe”, ya tabbatar.

Post a Comment

0 Comments