Yadda Maciji ya kashe wani mai kama Maciji har lahira a garin Samaru Zariya
Daga Idris Umar, Zariya
A ranar Lahadi da ta gabata ne wani magidanci kuma masani wajen kama macizai, Malam Hashimu Salisu, wanda ke zaune a unguwar Yar-Dorwa, Hayin Dogo Samaru, Zariya, ya rasa ransa bayan cizon da wani maciji ya masa yayin da yake kokarin kama shi a wata unguwa da ake kira Hanwa, cikin karamar hukumar Sabon Gari.
Wakilinmu ya kai ziyara gidan marigayin domin jin cikakken bayani daga bakin waÉ—anda suka kasance tare da mamacin a lokacin da lamarin ya faru.
Shaidar Ganau Malam Ibrahim Garba
Malam Ibrahim Garba, abokin sana’ar marigayin kuma ganau a wajen faruwar lamarin, ya bayyana cewa su biyune ke gudanar da sana’ar kama macizai. A cewarsa:
> “Mun samu kira daga wani gida a Hanwa cewa an hango maciji. Mun je cikin gaggawa. Ni na fara kai masa hannu, sai ya cizani a hannu. Da sauri na jefar da shi gefe. Abokin aikina, Malam Hashimu, ya tashi ya kama shi. Sai nan take ya sari shi a hannu – cizo mai Æ™arfi da guba sosai.”
A cewar Malam Ibrahim, bayan cizon, macijin ya gudu, kuma duk kokarinsu na nemansa ya ci tura.
> “Mun hau babur don koma gida. A hanya sai Malam Hashimu ya fara jin jiri. Nan da nan muka canza shawara muka wuce da shi asibitin koyarwa na ABU (ABUTH). A can suka masa allurar rigakafin cizo, amma kafin awa guda ya riga mu gidan gaskiya.”
Bayanan Rayuwar Marigayin
Malam Hashimu, direba ne a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, kuma yana sana’ar kama macizai a gefe domin taimaka wa al’umma. Ya rasu ya bar mata biyu da yara 24.
Binciken da aka gudanar
Rahotanni daga wajen bincike sun tabbatar da cewa karamin maciji ne ya sare marigayin, wanda ake kira "Jan Na suri", wanda duk da ƙanƙantarsa yana da guba mai matuƙar haɗari.
Dalilan da suka haddasa mutuwar cikin gaggawa:
1. Macijin ya cije shi ne a lokacin da jikinsa ke da zafin rana jininsa ya motsa sosai – hakan ya sa gubar ta shiga jikinsa cikin sauri.
2. Ba a tabbatar da irin macijin da ya sare shi ba kafin a ba da magani – wanda hakan ya sabawa Æ™a’idojin ba da maganin cizon maciji a kimiyyar maganin Bature.
3. Jinkiri kafin kai shi asibiti – wanda ya kara barazana ga lafiyarsa.
Wani É“angare na al’umma a yankin na Zariya na zargin cewa ba maciji na zahiri bane ya kashe marigayin suna ganin cewa wata halitta ce ko aljani musamman ganin yadda lamarin ya faru cikin sauri da kuma yadda aka kasa samun macijin bayan cizon.
A halin yanzu, jama’a da dama na tururuwa zuwa gidan marigayin don yin jaje da bayyana alhini kan wannan lamarin mai tayar da hankali.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan rahoto don kawo muku karin bayani a mako mai zuwa. Allah ya jiƙan Malam Hashimu, ya bai wa iyalansa haƙuri da juriya.
0 Comments