Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Taron ƙara wa juna sani da ƙungiyar KALM Community Initiative (KCI) ta shirya a ABU Zariya yayi armashi.


Taron ƙara wa juna sani da ƙungiyar KALM Community Initiative (KCI) ta shirya a ABU Zariya yayi armashi. 

Daga Idris Umar, Zariya 

Taron ya samu halartar matasa da dama, da malamai da jami’an gwamnati, inda aka tattauna hanyoyin da za a iya amfani da su wajen tallafawa matasa ta hanyar fasahar zamani.

A jawabin da shugaban hukumar KASITDA ya gabatar yayin taron, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano ta kuduri aniyar horas da matasa miliyan 1.5 daga shekarar 2025 zuwa 2027. Wannan horo zai mayar da hankali ne kan ƙwarewar fasahar zamani, kamar yadda zamani ke tafiya a yanzu.

Shirin na bai wa matasa dama a fannoni daban-daban kamar koyon amfani da na’urorin zamani, ƙirƙirar abun ciki (content creation), da kuma koyon coding. Ana raba horon zuwa matakai daban-daban: na farko, matsakaici da kuma na ƙwararru, domin kowa ya samu dama gwargwadon ƙarfinsa.

A halin yanzu, an riga an fara wannan horo a matakin gwaji inda matasa sama da 150,000 suka riga suka shiga. Daga cikinsu, fiye da 1,100 sun riga sun kammala karatu daga cibiyoyin koyon fasaha da ke Kano.

Ɗaya daga cikin muhimman shirye-shiryen da ke cikin wannan tsari shi ne HEAT Challenge, wanda ya shafi fannoni guda huɗu: lafiya, ilimi, noma da sufuri. Ana gayyatar matasa su kawo sabbin ra’ayoyi da hanyoyin fasaha da za a iya amfani da su wajen magance matsalolin da ke cikin waɗannan fannoni. Wadanda suka fito da mafita mafi kyau za su samu tallafin gwamnati, wanda ya haɗa da kuɗi da taimako don kafa kamfanonin fasaha.

KASITDA na da niyyar yaɗa wannan horo har zuwa makarantu da ƙauyuka, ba birane kaɗai ba. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa kowane matashi na da dama a cikin wannan gagarumin shiri.

A nata ɓangaren, ƙungiyar KCI ta bayyana cewa manufarta ita ce ta buɗe ƙofofin ci gaba ga matasa, musamman waɗanda ke da basira da ra’ayoyi masu kyau, amma ba su da kayan aiki ko dama da za su aiwatar da su. Tare da hadin gwiwar KASITDA, suna fatan ganin matasa sun samu horo da tallafi da zai taimaka musu su tsaya da kafafunsu a rayuwa.

A ƙarshen taron, shugabar da ta jagoranci shirin, Ms A’isha Muhammad, ta nuna matuƙar jin daɗinta bisa irin goyon bayan da aka nuna daga dukkan ɓangarori. Ta ce taron ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma an cimma abubuwan da aka tsara.

An gama taro lafiya, an tashi lafiya, kuma mahalarta sun bar wajen cikin farin ciki da ƙwarin guiwar cewa nan gaba mafi kyau na gabansu.

Post a Comment

0 Comments