Ziyarar girmamawa ga mai martaba sarkin Zazzau
Daga Idris Umar, Zariya
Bisa la'akari da Gundumuwar da Masarautar Zazzau take bayarwa da kuma irin nasarorin da take samu wajen Sassan tawa gami da gabatar da Sulhu a tsakanin al'umma, a yau Shugaban Kwamitin Kotun Bin Ba'asin Kananan Basussuka na Jihar Kaduna, Mai Shari'a Darius Hyet Khobo ya jagoranci membobin kwamitin wajen gabatar da ziyaran girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR a Fadansa.
A lokacin wannan ziyara Mai Shari'a Khobo ya gabatar da bayanai ayyukan kwamitin ga Mai Martaba Sarkin Zazzau da 'yan Majalisansa.
Ziyara ta sami karɓuwa sosai ga dukkan bangarorin biyu
0 Comments