Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC Sun Ziyarci Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda


Kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC Sun Ziyarci Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda 

A ranar Laraba 23 ga watan Yuli 2025, ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC suka ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, a gidan gwamnatin jihar Katsina domin yi mashi ta'aziyya da kuma jajanta mashi bisa wani haɗarin mota da ya rutsa da shi a yammacin ranar Lahadin da ta gabata a hanyar shi ta zuwa garin Daura.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodimma ne ya jagoranci tawagar domin kawo mashi ziyarar.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ne ya buɗe addu'a a lokacin taron, Gwamnonin jihar Benue Rev.Fr Hyacinth Alia da kuma Abdullahi Sule na Nasarawa suka rufe da Addu'a.

A jawabin shi Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar Hope Uzodimma ya bayyana irin haɗin kan ƴaƴan ƙungiyar tare da yin  ta'aziyyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma godiya ga Allah bisa samun lafiya da Gwamna Raɗɗa ya yi.

Ya cigaba da cewa a duk lokacin da ɗayan mu yake cikin farin ciki to zamu haɗu domin taya shi haka kuma idan bakin ciki ko alhini ne zamu taru mu taya juna.

A nashi ɓangaren Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya bayyana yayi matuƙar farin ciki ganin yadda ƴaƴan ƙungiyar suka ziyarce shi har gida tare da godiya bisa jajanta mashi da suka yi akan abun da ya faru da shi.

Gwamnan Dikko Radda ya kuma ce irin ɗawainiyar da shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu ya yi a lokacin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara nuna irin haɗin kan  ƴaƴan jam'iyyar ta APC.

A lokacin zaman akwai shugaban ƙungiyar gwamnoni Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrazaq Abdulrahman, sai sauran gwamnonin jam'iyyar APC na jihohin Benue, Nasarawa, Ekiti, Niger, Borno, Kogi, Kebbi, Sokoto, Ebonyi, Jigawa, Kaduna, Ogun, Ondo, sai kuma mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom a madadin gwamnan jihar.

Post a Comment

0 Comments