Kiwon lafiya a gidajen mu
Daga Idris Umar, Zariya
Daga Asibitin Sanata Suleiman Abdu kwari
Inda Uwar gidan Shugaban karamar Hukumar Sabon Gari Local Government Hajiya Husaina Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria(Algon Chairman kaduna State)ta jagoranci kaddamar Da Rabon Gidan Sauro wato Net ga Al,ummar karamar Hukuma ta Sabon gari a jihar Kaduna.
Hajiya Husaina Jamilu Abubakar Albani
Awajan taron Uwar gidan shugaban ta janyo hankalin Iyaye mata da suyin amfani da Gidan Sauron Yadda Yakamata don kiyaye Lafiyar Yaransu Da kamuwa da Zazzabin Cizan Sauro
" Muna Rokon Allah Yakarawa Yaranmu Lafiya harma da Iyayan Yaran baki ɗaya" inji ta
Malamai ne da masu anguwani sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya suka marawa taron baya.
An fara lafiya an tashi lafiya.
0 Comments