An fara raɗawa yara sunan shugaban karamar hukumar Sabon Gari ( Jamil Albani)
Daga Idris Umar Zariya
Wanin matashi mai suna malam Nazifi Muhammad da matarsa Fatima Muhammad wanda suke zaune a anguwar Kwangila Zariya ya raɗawa ɗansa da ya haifa suna Honorabul Jamilu Albani bisa wasu dalilai guda biyu.
Yayin da Hausa Media Reporters ke zantawa dashi a gidansa dake Anguwar Kwangila ya bayyana cewa, a kwanakin baya ya shiga cikin mawuyacin hali a sanadiyyar yadda aka koresu a wajan da yake gudanar da sana'ar neman abincinsa wato tashar (Kwangila Zariya Plyover) dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.
Matashin yace, an koresu ne da umurnin su koma sabuwar tashar yan'karfe kuma a lokacin matarsa nada ciki kuma kumi ya tsaya cik.
Amma sai ya duƙufa yin addu'a don Allah ya kawo masu sauki.
Yace, cikin ikon Allah sai Allah ya kawo masu canjin shugaban karamar hukuma a Sabon Garin wato Honorabul Abubakar Jamilu Albani da zuwansa sai yace kowa yazo ya ci gaba da kasuwancinsa amma abi doka don samun cigaban rayuwa.
Bisa haka ne komi nashi ya komo daidai.
Malam yace bisa haka ne yayi alƙawarin in har matarsa ta haihu zai nemi alfarma wajan matar nasa da iyayen su da su bashi damar ya sanyawa yaron da aka haifa suna Jamilu Albani kuma yace duk sun amince an raɗawa yaro suna Honorable Jamil Albani Samasu.
Bisa haka tuni shugaban ya aika da sakon godiya ga wannan bawan Allahn tare da jinjina.
Yanzu haka jinkiri na samun kyaututtuka daga ya'yan jam'iyyar APC masoya Honorabul Abubakar Jamilu Albani tare da yiwa yaron fatan alheri ga yaron da iyayensa.
Wani sako kuke dashi ga uban wannan yaron?
0 Comments