Honorabul Zakaria (Bomo) ya gabatar da kansa a matsayin ɗan takara
Daga Ummul- Kairi Nuhu, Zariya
Al'ummar Gundumar Basawa constituancy da suka haɗa gudumomi hudu ne 4 sukayo faran ɗango don marawa ɗansu baya a wajan tsai dashi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltarsu.
Gundumomin sun haɗa da Bomo word Basawo word har Samaru word, da jama'a word .
Mata da maza da ƙananan yara dattawa da matasa ne suka fito domin marawa Honorabul Zakariyya Isah Bomo baya a lokacin.
Dubban jama'a ne suka taru domin rakashi ofishin jam'iyar APC me albarka don gabatar da kansa ga iyayen jam'iyya da kuma shaida masu cewa yana neman takarar ɗan majalisar jihar Kaduna mewakiltar basawa constituancy karkashin jagorancin tafiyar Gwamnan malam Uba Sani da Malam Abubakar Kamilu Albani Samaru.
Lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin rakiyar ya faɗi kudirinsa kamar haka.
Yace yana da burin karfafa matasa a ɓangaren ilmi, ya kuma tabbatar da cewa zai kula da harkar lafiya da jin daɗi da walwala na al'umma karamarsa hukumar Sabon Gari.
Karshe ya roki matasa da subi doka da oda yayin gudanar da zaɓuƙan
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.
0 Comments