Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamnan Jihar Kaduna Ya Kaddamar Da Kwamitin Raba Takin Zamani, Kyauta Ga Manoma 100,000 A Fadin Jihar Kaduna


Gwamnan Jihar Kaduna Ya Kaddamar Da Kwamitin Raba Takin Zamani, Kyauta Ga  Manoma 100,000 A Fadin Jihar 

Gwamnan Jihar Kaduna, Senator Uba Sani, CON, ya kaddamar da wani kwamiti mai kunshe da wakilai daga bangarori daban-daban don tabbatar da gaskiya da inganci wajen rabon Tirellar taki fiye da 300 ga manoma 100,000 a fadin jihar. Wannan shiri wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar wajen kara inganta wadatar abinci, tallafa wa rayuwar al’ummar karkara, da bunkasa harkar noma a cikin al’umma.

A karkashin rukunin kananan manoma, kowane mai cin gajiyar wannan tallafi zai karɓi buhuna biyu na taki kyauta. A rukuni na biyu, manyan manoma (commercial farmers) za su amfana da wani shirin tallafin kayan noman da aka keɓe musamman domin su. Za a sayar musu da takin da ragin kashi 40% cikin dari. Wannan tsari an kirkiro shi ne don karfafa habakar kasuwancin noma, samar da ayyukan yi a sarkar harkar noma, da kuma rage farashin kaya ta hanyar saukaka kudin kayan shuka.

Baya ga wannan tallafi na kayan shuka, Gwamnatin Jihar Kaduna za ta sanya manoma 100,000 a tsarin inshorar hatsarin amfanin gona. Wannan mataki zai taimaka wajen kare amfanin gonar manoma daga barazanar kwari, cututtukan amfanin gona, da kuma sauyin yanayi da ke da nasaba da dumamar yanayi (climate change). Wannan wani bangare ne na kudurin gwamnatin jihar wajen gina tsarin noma mai dorewa da kariya.

Domin tabbatar da sahihanci, gaskiya da kulawar al’umma, za a gudanar da rabon takin da sa ido a matakin jiha da kananan hukumomi, tare da hadin gwiwar wakilai daga bangarori kamar haka: gwamnati, ‘yan kasuwa, kungiyoyin fararen hula, shugabannin gargajiya da na addini, kungiyoyin kwadago, hukumomin tsaro, da kuma cibiyoyin yaki da cin hanci da rashawa.

Wannan tsari na hadin gwiwa yana nuna jajircewar Gwamnatin Jihar Kaduna wajen tabbatar da sauyi mai inganci a fannin noma, ci gaban karkara, da kuma samar da tsarin abinci mai dorewa.

                

Post a Comment

0 Comments