A ranar Litinin 7 ga watan Yuli 2025, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya halarci bikin buɗe Kamfanin haɗa garin Masara da Madarar shanu mai suna TFK (The Farm Katsina LTD) mallakin Sardaunan Katsina Amb Ahmed Rufa'i, a garin Shinkafi cikin ƙaramar hukumar Katsina.Da yake gabatar da jawabi a wajen taron gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya yaba ma Ambasada Ahmed Rufa'i, bisa assasa katafaren kamfanin wanda zai taimaki al'ummar jihar Katsina ta fuskar kasuwanci, samar da abun yi, bunƙasa tattalin arziki, da sauran su.
Ya cigaba da cewa wannan abun a yaba ne kuma ayi alfahari, "sabo da idan da yaso zai iya buɗe shi wani garin da ribar da zai samu ƙila ma tafi ta nan amma ya zaɓi ya yi shi a nan Katsina domin kishin garin shi da jihar shi baki ɗaya" cewar Gwamna Raɗɗa.
Gwamnan ya kuma yi bayanin irin nasarorin da gwamnatin shi ta samu a ɓangaren noma tun bayan kafuwar ta wanda suka haɗa da samar da cibiyar kayan aikin gona na zamani, wadatar da takin zamani, raba kayan noman rani da suka haɗa da famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana da kuma na feshi, da sauran su.Daga ƙarshe ya yi kira ga sauran al'ummar jihar Katsina, da suke da damar buɗe kasuwanci da suyi hakan domin taimaka ma jihar Katsina, wajen bunƙasa tattalin arziki, rage yawan zaman banza, da kuma bunƙasa kasuwanci a jihar.
Tun da fari shugaban gonar ta TFK The Farm Katsina, Amb Ahmed Rufa'i, ya fara da bayyana irin yadda ya fara aikin samar da gonar, wanda ya bayyana tun a shekarar 2006 zuwa 2007 ya fara lokacin da yake wani aiki na musamman a ƙasar Sudan, a hankali yau gashi ya kammala aikin.
Amb Ahmed Rufa'i, ya kuma nuna godiyar shi ga Babban bankin Najeriya CBN, bisa gudummuwar da ya bashi wajen samar da kamfani haɗa garin Masarar, ya kuma gode ma bankin Eco bisa irin tashi gudummuwar, ya kuma gode ma kamfanoni da dama da suka taimaka mashi
0 Comments