Amfanin kananan sana'o'i ga talaka
Daga Abubakar Musa
Sana'a, babba ko karama, na da matukar muhimmanci wajen cigaban tattalin arzukin al'umma da kasa baki daya.
Kananan sana'o'i, wadanda sana'o'i ne da za a iya farawa ba lallai sai da babban jari ba, na iya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da talauci, rashin aikin yi da sauran matsalolin tattalin arzuki da al'ummar kasa, musamman talakawa, ke fuskanta.
Idan an yi la'akari da cewa manyan 'yan kasuwa attajirai wadanda suka yi fice a duniya, kasa, jihohi, kananan hukumomi ko a yankunansu da garuruwansu na jajircewa wajen ganin cigaba a kasuwancinsu domin sanin muhimmancin yin hakan, za a yarda cewa talakawa bai kamata su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun koyi wata sana'a suma kuma sun jajirce domin neman rufin asiri a rayuwarsu.
Muhimmancin kananan sana'o'i ga talaka suna da yawa, na daya za mu iya cewa akwai dogaro da kai, domin kuwa mutanen da ke da sana'a za ka samu sun iya dogaro da kansu wajen yin hidimomi na rayuwarsu da ta iyalinsu da dama ba tare da neman taimako ko kuma jiran wasu su yi masu wata hidima ta rayuwa ba.
Wani muhimmancin kananan sana'o'i ga talaka shine yin sana'o'in ba kawai tattalin arzukinsu ya ke ingantawa ba amma har da tattalin arzukin kasarsu, domin kuwa yayin da mutane suka kasance suna yin kananan sana'o'i to rashin aikin yi zai ragu, mutanen da suke talakawa za su ragu kuma masu wadata su karu wanda hakan babban taimako ne ga tattalin arzukin kasa.
Kananan sana'o'i har wa yau suna da muhimmanci ga rayuwar matasa domin kuwa wasu matasan da suka afka cikin miyagun dabi'u na sace-sace, shaye-shaye, fadace-fadace da sauransu sun afka ne sakamakon rashin aikin yi, saboda haka a lokacin da matasa suka rungumi kananan sana'o'i domin samun rufin asiri a rayuwarsu za ka samu irin wadancan dabi'u sun ragu matuka a tsakaninsu, hakan kuma zai taimaka wajen samun matasa na gari wadanda sune manyan gobe.
Saboda haka, kananan sana'o'i abu ne da ya kamata mutane su ruke da kyau su kuma mayar da hankali a kai sosai ganin cewa alfanun hakan na da yawa ba kadan ba.
Domin samun nasara, ana bukatar kwarewa a sana'ar da mutum ya zaba zai yi, akwai bukatar yin gaskiya, ruke amana da mutunta juna, akwai bukatar jajircewa da mayar da hankali da sauran kyawawan dabi'u domin samun nasara a duniya da lahira.
A bangaren gwamnati, akwai bukatar samar da shirye-shirye domin koyar da kananan sana'o'i ga 'yan kasa, maza da mata, samar da jari, kyawawan tsare-tsare domin shirye-shiryen gwamnatin su kai ga nasara da sauransu.
0 Comments