Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKA GABATAR DA TARON SAUKAR KARATUN A FUDIYYA KUDAN


YADDA AKA GABATAR DA TARON SAUKAR KARATUN A FUDIYYA KUDAN 

Tun Da Misalin Karfe 9:30 Na Safiyar Yau Alhamis 1st May, 2025 Filin Taron Ya Fara Daukar Baki Mahalarta Taron Walimar Saukan Alkur'ani Na Dalibai Kimanin 37 Da Allah Ya Azurta Da Sauke Alkur'ani Mai Tsarki. Taron Ya Sami Halartar Dinbin Al'umma Kamar Alarammomi, Wakilan Yan Uwa, Sarkin Kudan Alhaji Muhammad Bello Haladdu, Limamai, Masu Unguwanni, Bangarorin Tsaro Da Sauran Baki Maza Da Mata Yara Da Manya.

An Fara Bude Taron Da Addu'a, Karatun Alkur'ani Mai Tsarki, Jawabin Maraba Da Mahalarta, Bayani Akan Halin Da Makarantar Ke Ciki, Baitocin Yabo Ga Annabi MUHAMMAD Da Iyalan Gidan Sa (as) Da Faretin Daliban Madarasatul Fudiyya, Wanda Wakilin Yan Uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Ya Karbi Wannan Faretin.

Bayan Nan Sai Aka Shiga Gabatar Da Karatun Gwaji Ga Dalibai Masu Sauka, Wanda Aka Kasa Daliban Zuwa Gida Biyar. Kowane Gida Aka Gabatar Da Wani Alaramma Daga Wajen Harka Domin Gwada Daliban. Sannan Malam Abdu'aziz Yahya Ya Jagoranci Gabatar Da Karatun Sauka Ga Daliban.

Sheikh Abdulhamid Bello Zaria Shine Ya Kasance Babban Bako a Wajen Wannan Taro Mai Albarka. Kuma Ya Gabatar Da Takaicen Nasiha Da Jan Hankali Ga Dalibai Da Sauran Al'umma Akan Wajibcin Neman Ilimi Musamman Na Alkur'ani, Da Sauran Fannonin Ilimi. Shehin Malamin Ya Yi Kokari Wajen Kwadaitar Da Al'umma Matsayi Daraja Da Tasirin Mahaddacin Alkur'ani, Yana Mai Kawo Hujjoji Daga Daga Hadisan Manzon Allah (S).

Bayan Kammala Jawabin Sheikh Din, An Bawa Iyaye, Dangi Da Makusantan Daliban Dama Domin Shigowa Su Taya Yan Uwan Su Murna a Wannan Waje. Yan Uwa Da Dangi Kuwa Suka Yi Ta Ruwan Nairori Ga Wadannan Dalibai.

A Kusa Da Karshe An Gabatar Da Hotuna Na Musamman Tare Da Dalibai Da Manyan Baki Da Sauran Iyaye Da Dangi. An Kuma Gabatar Da Kwarya-kwaryan Kaddamar Da Kalandar Masu Saukar.

A Karshe Aka Yi Addu'a Aka Sallami Kowa, Sannan Aka Raba Abincin Walima Ga Mahalarta.


3rd Zulkada, 1446
1st May, 2025

Post a Comment

0 Comments