Zanga-zangar Ma'aikata Ta Barke a Birnin Abuja
Malaman Firamare da na sauran ma'aikatan Ζ™ananan hukumomin Abuja kenan, a yau Alhamis ke gudanar da zanga-zangar lumana a kan tituna, kan rashin biyan su mafi Ζ™arancin albashi, da sauran haΖ™Ζ™oΖ™in da suke bin shugabannin Ζ™ananan hukumomi 6 da ke Abuja.
Sun gudanar da zanga-zangar ne Ζ™arΖ™ashin Ζ™ungiyar malaman makaranta ta NUT, da kuma Ζ™ungiyar ma'aikatan Ζ™ananan hukumomi ta NULGE.
0 Comments