Dan majalisar wakilai Abbas ya baiwa NUJ Shiyar Zariya motar Bas mai kujerar 10
Daga Idris Umar, Zariya
Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Rt. Honorabul Abbas Tajuddeen, ya bai wa Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Zariya, wata mota kirar Sharon mai kujeru 10 domin sauƙaƙa musu aikin su na yau da kullum.
An gabatar da wannan kyauta ce a ranar Lahadi a ofishin mazabar Kakakin da ke Zariya, inda Babban Jami’in HulÉ—a da Mazaba na Kakakin, Alhaji Isma’il Mohammed Yesco, ya miÆ™a takardar mallakar motar ga shugabannin kungiyar.
A yayin gabatar da motar, Alhaji Yesco ya bayyana cewa wannan taimako na daga cikin manufar Kakakin na Æ™arfafa alaÆ™a mai kyau da ‘yan jarida tare da nuna damuwa kan matsalolin da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu.
“Rt. Honorabul, Abbas Tajuddeen ya damu da halin da 'yan jarida ke ciki a Zariya, musamman rashin motar aiki. Wannan kyauta za ta taimaka gaya wajen inganta ayyukansu da sauÆ™aÆ™a musu gudanar da aikin jarida,” in ji shi.
Da yake karɓar kyautar a madadin NUJ reshen Zariya, Mataimakin Shugaban reshen, Kwamared Sani Aliyu, ya nuna matuƙar farin ciki da godiya bisa wannan tallafi, yana mai cewa wannan ne karo na farko da aka bai wa 'yan jarida a Zariya irin wannan gudummawa mai muhimmanci.
“Ina mai tabbatarwa Kakakin cewa wannan kyauta ta faranta mana rai matuÆ™a, ta kuma Æ™ara mana kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukanmu. Tabbas mun dade muna jiran irin wannan lokaci,” in ji shi.
Kwamared Aliyu ya ƙara da cewa wannan gudummawa ta Kakakin ta magance kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin su da suka shafi harkar sufuri, yana mai tabbatar da cikakken goyon bayan kungiyar ga Kakakin tare da ci gaba da rufe dukkan ayyukansa a kullum.
0 Comments