Header Ads Widget

Responsive Advertisement

RT Hon. Garba Datti Muhammad (Babawo) Ya Raba Tallafin Azumi a Zariya


RT Hon. Garba Datti Muhammad (Babawo) Ya Raba Tallafin Azumi a Zariya.

Daga Umar Idris, Zariya 

A cikin satin da ya gabata RT Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) mataimakin shugaban jamÉ“iyar APC Shiyar Arewa maso yamma kuma shugaban Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Kasa (NESREA) ya raba kayan tallafin abinci ga al’ummar karamar hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

An gudanar da taron rabon kayan abincin ne a babban gidansa da ke GRA Sabon Gari, 

shugabannin jam’iyyar APC na mazabu, maza da mata, da sauran jiga-jigan siyasa suka halarci gurin kaddamar da rabon tallafin.

Shugaban Kungiyar Ciyamomin Ƙananan Hukumomi na Jihar Kaduna (ALGON), Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru, shi ne ya ƙaddamar da rabon a madadin RT Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) da mai girma Sanata Uba Sani.

A yayin jawabinsa, Shugaban Æ™aramar Hukumar ya yabawa RT, Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) bisa Æ™okarinsa na kawo ci gaba a Ƙaramar hukumar Sabon Gari musamman ta hanyar tallafawa al’umma.

Shugaban ya bayyana wannan tallafi a matsayin abin alfahari, musamman a wannan lokaci na azumi.

Haka kuma, ya jinjinawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna, yana mai cewa, "A yanzu haka da bazar Sanata Uba Sani.muke rawa," tare da yin addu’ar Allah ya ba shi nasara a dukkan abin da yake nema.

A binciken da wakilanmu suka  gudanar, an tabbatar da cewa RT Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) ya raba buhunan shinkafa akalla 2,000 mai nauyin 50kg da 25kg domin rage wa jama’a dauyin da ke kansu.

Daya daga cikin waÉ—anda suka amfana, da tallafin Malama Aisha, daga anguwar muciya ta bayyana godiyarta tare da yin addu’a ga RT Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) da Sanata  Uba Sani da Honorabul Abubakar Jamilu Albany Samaru, da dukkan shugabannin jam’iyyar APC da suka bada gudunmawa a wannan shiri.

Shugaban ya ƙara da cewa wannan tallafi ya nuna jajircewar RT Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) da sauran jiga-jigan siyasa wajen tallafawa
 al’ummar Jihar Kaduna, musamman a lokutan da ake bukatasa

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments