Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Isra'ila ta sake kashe wani dan jarida a Gaza


Isra'ila ta sake kashe wani dan jarida a Gaza

Isra'ila ta sake kashe wani dan jarida Bafalasdine a Gaza.  Hossam Shabat na Al Jazeera shi ne dan jarida na biyu na Falasdinu da aka kashe a cikin sa'o'i 24 wanda ya kawo adadin 'yan jarida da ma'aikatan yada labarai da aka kashe a Gaza sama da 170 - a cewar kwamitin kare 'yan jarida.

 Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Isra'ila ta kai hari kan wani asibiti, inda ta kashe fararen hula da sunan ta nufi wani jami'in Hamas. 

 Hakan na faruwa ne mako guda bayan da ta kashe daruruwan mutane da suka hada da mata da yara a wasu hare-hare da aka kai a gabar teku bayan karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'iln ta yi. 

 Babu ɗayan waɗannan da ke samun kulawar manyan kafofin watsa labarai a cikin Amurka ko kasashen yamma.  Kuma ba kasafai kowa ke magana ba in ban da Isra’ilawa kan dalilin da ya sa Netanyahu ya ci gaba da abin da mutane da yawa ke cewa yakin kisan kare dangi ne don dakile rugujewar siyasarsa da zargin cin hanci da rashawa da kw bibiyarsa.

Post a Comment

0 Comments